Mai ɗakin shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta gana da Oluremi Tinubu, matar shugaban Nijeriya, inda suka tattauna kan ayyukan da ta ƙaddamar don inganta rayuwar mata da matasa.
A ganawar tasu, sun duba damarmakin haɗa gwiwa tsakanin ofisoshinsu kan waɗannan ayyuka na ci gaba.
Emine Erdogan, matar shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ta karɓi baƙuncin Oluremi Tinubu, matar shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, wadda ta ziyarci Istanbul bayan da ta samu gayyata daga takwararta ta Turkiyya.
Oluremi Tinubu ta gode wa Emine Erdogan kan gayyatarta da karɓar baƙuncinta. Ita ma uwargidan Erdogan ta taya shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da matarsa, murnar lashe zaɓen da ya gabata a ƙasar.
Uwargidan Erdogan ta bayyana cewa Nijeriya ƙasa ce mai ɗumbin arziƙi da al'adu da albarkar yawan jama'a, kuma ta jaddada cewa Nijeriya babbar ƙawa ce mai muhimmanci ga Turkiyya.
Dangantakar gaskiya
Uwargida Emine Erdogan ta ce ta yi imanin cewa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu za ta ci gaba da haɓaka ƙarƙashin mulkin shugaba Tinubu, inda ta yi nuni kan cewa Turkiyya ta kafa danganta ta gaskiya da ƙasashen Afirka.
Ta kuma ce, ta hanyar wannan fahimta tsakaninsu, Turkiyya za ta samar da duk wani tallafi ga ƙasashen Afirka, kuma za su yi aiki tare.
Da take mayar da jawabi, Uwargida Oluremi Tinubu ta ce ta lura uwargidan Turkiyya tana nuna muhimmiyar damuwa kan tallafa wa Afirka.
Ita ma Emine Erdogan ta bayyana wa Oluremi Tinubu bayanai kan shirinta na "Gidan Al'adu da Kayan Fasahar Afirka", inda ake sayar da kayayyakin da matan Afirka suke sarrafawa, kuma ake mayar da kuɗaɗen ga mata a ƙasashen Afirka.
Da take jawabi kan arziƙin da Nijeriya take da shi a ɓangaren al'adu sakamakon ɗaruruwan ƙabilu da harsunan da take da shi, Oluremi Tinubu ta ce za ta yi murna kan shirin Emine Erdogan na kayayyakin Afirka.
A yayin ganawar, Emine Erdogan ta faɗa wa Oluremi Tinubu game da littafan da ta wallafa game da Afirka, "My Travels to Africa", "African Proverbs" da kuma shirye-shiryenta na wallafa littafi kan salon girkin na "African Cookbook".
Saka Afirka a zuciya
"Mun gode wa Emine Erdogan kan damuwarta kan Afirka", cewar Oluremi Tinubu inda ta ƙara da cewa Uwargida Emine Erdoğan ta sanya Afirka a zuciyarta duk da cewa ita ba haifaffiyar Afirka ba ce.
Ta kuma bayyana gamsuwarta da yabawa kan ƙoƙarin uwargidan Erdogan na haɓaka al'adun Afirka. A taron nasu, sun tattauna kan damarmakin haɗin-kai da ayyukan da aka ƙaddamar kan inganta rayuwar mata da matasa.
Uwargidan Tinubu ta bayyana tasirin ayyukan da aka gudanar a fannoni da dama, musamman haɓaka rayuwar mata da tallafawa jama'a.
Sun kuma tattauna kan muhimmancin ilimi, inda Oluremi Tinubu ta yaba wa cibiyar Yunus Emre Institute, wadda shugaba Erdogan ya buɗe a ziyararsa ta ƙarshe zuwa Nijeriya, wadda cibiya ce da ke samar da damarmaki.