Wuraren da aka kai wa harin sun hada da matsugunan soji, amma ba a yi wani dogon bayani ba.

1638 GMT — Kungiyar Hizbullah ta Labanan ta kaddamar da hare-hare 19 daban-daban a lokaci guda a arewacin isra'ila da ke iyaka da Labanan, in ji wata majiya da ta rawaito babban jami'in Hizbullah na bayyana hakan.

Majiyar ta ce wuraren da aka kai wa harin sun hada da matsugunan soji, amma ba a yi wani dogon bayani ba.

Karin sabbin bayanai

1721 GMT — Blinken zai yi magana da Isra'ila kan 'kwararan matakai' don rage cutuwar fararen hula

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce zai bukaci Isra'ila da ta dauki 'kwararan matakai' don rage cutuwar fararen hula a Gaza a yayin da ya fara ziyara zuwa Gabas ta Tsakiya game da rikicin.

"Za mu tattauna kan kwararan matakan da za su rage cutuwar maza, mata da yara kanana a Gaza," in ji Blinken yayin zanta wa da manema labarai a Sansanin Sojin Sama na Andrews a lokacin da yake tashi zuwa wjaen kasar.

"Wannan wani abu ne da Amurka ta himmatu a kai," ya fadi haka kwana guda kafin ya gana da Firaminista Benjamin Netanyahu.

1514 GMT — Umarnin kwashe mutane daga asibitin Gaza ya jefa daruruwan marasa lafiya cikin hatsari: WHO

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce tirsasa kwashe mutane daga asibiti a Zirin Gaza zai jefa rayuwar daruruwa marasa lafiya cikin hatsari.

“An umarci asibitoci ashirin da uku da ke Zirin Gaza da arewacn yankin kansu kwashe marasa lafiyan da ke wajen, wanda hakan za jefa rayuwar daruruwan marasa lafiyar cikin hatsari,” in ji Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Tedros ya ce “Mun rasa me za mu ce don bayyana mummunan yanayin da ake shiga a Gaza.”

1558 GMT —Isra’ila ta zargi kungiyar Iran da taimaka wa Hezbollah wajen kai hare-hare a kan iyaka

Rundunar sojin Isra’ila ta zargi kungiyar Iran mai dauke da makamai da taimaka wa Hezbollah da ke Labanon wajen kai hare-hare a kan iyaka.

A wata sanarwa, kakakin rundunar sojin Avichai Adraee ya ce mambobin Dakarun Imam Hosseini sun isa ga Kudancin Labanan don bayar da taimako ga Hezbollah.

Kakakin ya ce kungiyar da aka fara kafa ta a Siriya, ta yi arangama da dakarun Isra’ila a kan iyaka a ‘yan makonnin da suka gabata.

Adraee ya ce “Hezbollah da mayakan Imam Hossein na tirsasawa Labanon fuskantar kalubale saboda Hamas.”

1526 GMT — Dakarun Isra'ila sun kutsa cikin Gaza sosai ta ƙasa — Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce dakarun Isra'ila sun sake kutsawa can cikin Gaza a hare-haren da suke kai wa ƙungiyar Hamas a rabin arewacin Gaza.

"Muna tsaka da yaƙin. Muna samu nasarori sosai kuma mun shiga cikin Gaza. Mun wuce waje-wajenta," in ji Netanyahu a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar. Sai dai babu wani ƙarin bayani kan hakan.

1401 GMT — Gomman mutane sun mutu a harin Isra'ila kan wata makaranta da sansanin gudun hijira na Bureij a Gaza

Ƙungiyoyin agaji da ke aiki a yankin Gaza da ke cikin ƙawanya sun ce aƙalla gawar mutum 15 aka gano a ƙarƙashin baraguzai bayan da Isra'ila ta kai wani harin sama a kan sansanin ƴan gudun hijira na Bureij.

Kazalika wasu mutum 27 din sun mutu a wani harin daban da aka kai kan wata makaranta mallakar Majalisar Dinkin Duniya, a cewar Ma'aikatar Lafiya da Gazan.

1244 GMT — Isra'ila ta kai hare-haren sama fiye da sau 12,000 cikin Gaza tun 7 ga Oktoba

Hare-haren da Isra'ila ke kai wa ta ƙasa a Gaza suna yin cikas ga ayyukan agaji da ake kai wa mutum kusan 300,000, in ji MDD. Hoto: AA

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ƙasar ta kai hare-haren sama fiye da sau 12,000 cikin Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba.

Wata sanarwa ta ce an kai harin kan dubban wurare a yayin wadannan hare-hare.

A wannan makon, rundunar sojin Isra'ila ta faɗaɗa kai hare-harenta ta sama da ta ƙasa cikin Gaza, wacce ke cikin uƙubar hare-haren Isra'ilan tun bayan wani harin ba-zata da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

TRT Afrika da abokan hulda