Babbar kotun Faransa ta amince da matakin gwamnatin kasar na haramta wa dalibai sanya abaya a makarantun kasar.
Kotun ta yi watsi da karar da wata kungiyar Musulmai ta shigar tana kalubalantar matakin, wanda gwamnatin Emmanuel Macron ta dauka a watan jiya.
Kotun ta ce haramta sanya abaya ba nuna wariya ba ne ga Musulmai.
"Wannan haramcin bai keta hakkin gudanar da addini da neman ilimi … ko kuma tsarin nuna wariya ba,” in ji sanarar da kotun ta fitar.
Ranar 31 ga watan Agusta, Vincent Brengarth, lauyan kungiyar Musulmai ta Muslim Rights Action (ADM), ya shigar da kara a gaban kotun inda ya bukaci ta dakatar da gwamnati daga haramta sanya abaya, matakin da ya ce ya keta ‘yanci daban-daban na dan adam.
Labari mai alaka: Makarantun Faransa sun kori Musulmai da suka ki cire abaya
A farkon makon nan Ministan Ilimin Faransa Gabriel Attal ya ce dalibai kusan 300 ne suka bijire wa dokar haramta sanya abaya ranar Litinin lokacin da aka sake bude makarantu bayan an yi hutu.
Yawancinsu sun amince su sauya tufafin da ke jikinsu amma 67 sun ki yarda su cire abaya, kuma an kore su gida, a cewar ministan.
A watan jiya ne gwamnati ta sanar da haramta sanya abaya a makarantu, tana mai cewa Faransa kasa ce da ke raba harkokin kasa da na addini.
Matakin ya faranta ran masu tsattsauran ra'ayi amma masu sasaucin ra'ayi sun ce hakan take hakkin mata Musulmai ne.