Mai shigar da ƙara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC yana neman sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da ministan tsaron ƙasar Yoav Gallant da shugabanni uku na Hamas  saboda laifukan cin zarafin ɗan-adam. / Photo: Reuters

Daga Sylvia Chebet

"Da babu gara ba daɗi."

Yayin da lauyan kare haƙƙin bil-adama Francis Boyle ya ambata kalaman nan, da yake martani kan mai shigar da ƙara na ICC, Karim Khan don neman sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaron ƙasar Yoav Gallant, kan laifukan cin zarafin ɗan'adam, da alama ya faɗi zuciyar kowa da yaƙin Gaza yake baƙantawa.

Hotuna masu sosa rai na waɗanda aka jikkata - yara da iyaye masu kukan alhini yayin da suke tono ɓaraguzan gini da hannayensu suna tunanin samun masu sauran rai, da Falasɗinawa da aka garƙame a wuraren da ba a san ina ne ba, kum ba su san makomarsu ba, — Gaza ta zamo wata jahannama ce a duniya a watanni bakwai da suka gabata.

Yayin duk wayewar gari ake fargabar samun ƙaruwar mamata da asarar dukiyoyi, ana samun ƙaruwar matsin lamba kan kotun don ta ɗauki mataki.

"Me kake jira Mista Khan?" in ji jakadan Libya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Taher El-Sonni, da yake tambayar mai shigar da ƙarar na ICC. Ya ƙara da cewa, "Shin ba ka ganin ta'asar da ake aikata a kan farar-hula? Duniya na jiran ICC ta nuna ƙarfin hali da bayar da sammacin kama jami'an gwamnatin Isra'ila".

Khan ya ce yana da ƙwararan hujjoji da ya amince cewa Netanyahu da Gallant da shugabannin Hamas uku sun aikata laifukan yaƙi, da kuma laifukan cin zarafin dan adam a zirin Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba na 2023.

Gwamnatin Netanyahu ta yi amfani da shammatar da Hamas ta yi wa Isra'ila ranar 7 ga Oktoba, wanda a cikinsa ta kashe mutum 1,200, a matsayin dalilin ƙaddamar da hare-haren bindiga da bama-bamai da makamai ma su linzami a Gaza tun daga 8 ga Oktoban bara zuwa yau.

Khan ya ce Isra'ila ta gaza yin aiki da dokokin kula duniya kan kula da dan adam.

" Wannan na nufin Isra'ila ta zaɓi ta cimma manufarta a Gaza - da suka haɗa da janyo mutuwa dagangan da haifar da yunwa, da tsananin azabtarwa da ji wa mutane munanan raunuka ga jiki da lafiyar jikin fararen hula - dukkansu laifuka ne," kamar yadda mai shigar da ƙara ya gabatar.

Boyle, wanda ya gamsar da Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya amince da hurumin kotun ta ICC, yana cewa an aikata wa Falasɗinawa laifukan yaƙi da cin zarafi tun daga fara Nakba ko bala'i a 1948.

A shekaru 15, duk da miyaguna laifuka da kisan ƙare dangi, da laifukan yaƙi da cin zarafi, masu shigar da ƙara uku masu zaman kansu sun kasa yin komai don taimakon Falaɗinawa har yau. Don haka a yanzu muna godiya, kamar yadda ya shaida wa TRT Afirka.

Me zai faru nan gaba?

Buƙatar ta masu shigar da ƙarar na ICC za ta je ne ofishin share fagen fara shari'a, inda alƙalai uku daga Romania da Mexico da Benin za su yi yanke hukunci ko an cika sharuɗan bayar da sammacin.

Sai dai alƙalan ba su da wani wa'adi da za su yanke hukunci idan za su za su ba da sammacin kuma yaushe za su bayar da shi. A baya dai, an san alƙalan da shafe fiye da wata ɗaya zuwa watanni da dama kafin su yanke hukunci a kan irin wannan buƙata.

"A lokacin da aka buƙaci ba da sammacin kama Shugaban Rasha Vladmir Putin da wasu jami'an gwamnatinsa, na tabbatar da cewa kun samu wannan cikin mako hudu," kamar yadda Boyle ya tuno abin da ya faru.

Farfesan a kwalejin shari'a na jami'ar Illinois a Amurka ya amince cewa siyasar diniya za ta iya yin tasiri kan hukuncin da alƙalan za su yanke. "Ina da yaƙini cewa Amurka da Isra'ila da masu Yahudawa za su sa yi matuƙar matsa lamba kan alƙalan na ICJ. "Don haka za mu jira mu ga abin da zai faru a nan."

Tuni wasu 'yan majalisar Amurka biyu daga jami'iyyar Republican suka gabatar da "Ƙudirin Dokar Haramta Kotun" don sanya takunkumi ga jami'an ICC da suka bibiyar jami'an ƙasar ta Amurka ko kuma ƙawayenta, ciki har da Isra'ila.

"Ina ƙara jaddada cewa duk wani yunƙuri na na hawa wa ko barazana ko murɗa jami'an kotun ta hanyar da ba ta kamata ba dole a tsayar da shi nan take," kamar yadda babban mai shigar da ƙara na ICC Imran Khan ya jadda ranar 20 ga Mayu lokacin da yake bayyana matakin da ya yanke.

Idan har alƙalan suka amince cewa akwai "gamsassun hujjoji" da za su amince cewa an aikata laifukan yaƙi sannan an ci zarafin jama'a, za su ba da sammacin.

Kotun ICC ta bayar da sammacin kama mutane sau 46 sai dai mutum 17 ana nemansu ne bayan sun tsere. Hoto: AA

Tsaka-mai-wuya

Babbar tambaya ta gaba ita ce: Ko za a kama Netanyahu da Gallant da shuganannin Hamas?

Yarjejeniyar Rome Statute wacce ta kafa kotun ta tilasta wa duka ƙasashe 124 da suka sa amince da kotun su kama mutum su miƙa shi - idan kotun ta ba da sammacinsa - idan suka suka saka ƙafarsu a ƙasar.

ICC ba ta da 'yan sanda da za su kama waɗanda ake zargi. A maimakon haka, yarjejeniyar kafa kotun ta tilasta wa ƙasashe mambobin kotun su kama wanda ake zargi su miƙa wa kotun idan ya shiga ƙasarsu. To amma ƙasashe da dama sun yi watsi da wannan nauyin amma duka-duka sai dai a ɗan yi musu abin da bai kai ya kawo ba.

Idan kotun ta ta amince da buƙatar masu shigar da ƙarar, shugabannin Isra'ila da na Hamas za su shiga jerin sunayen mutane da dama da ake zargi da aikita laifuka amma har yanzu ba a kama su ba.

Idan Kotun ICC ta bayar da sammacin kama shugabannin Isra'ila da na Hamas, tafiye-tafiyensu za su taƙaita ko da yake suna iya yin bulaguro zuwa ƙasashe ƙawayensu. / Hoto: AA

Shugabannin Isra'ila suna samun goyon bayan Amurka kuma za su iya tafiya ƙasar su koma gida salin-alin.

Mutanen da ake nema

Kotun ta ICC ta ba da sammacin kama mutum 46 tun daga lokacin da aka kafa ta a 2002. Shafin intanet na kotun ya ce an tsare mutum 21 a wajen tsare mutane na kotun da birnin Hague, sakamakon haɗin kan da ƙasashe ke bayarwa, kuma sun bayyana a gaban kotun. 17 daga cikinsu har yanzu ba su shiga hannu ba. An sokr tuhumar da ake yi wa mutum bakwai saboda sun mutu.

Manyan mutanen da ke cikin waɗanda kotun ke nema sun haɗa da Shugaban Rasha Bladmir Putin, wanda ake nema saboda yaƙi a Ukraine. A watan Maris ɗin 2023 kotun ta ba da sammacin kama shi.

Tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir yana fuskantar tuhumar cin zarafin jama'a da yaƙi a yankin Darfur, inda aka ƙiyasata cewa an kashe kimanin 300,000. An ba da sammacin kama shi a 2009 lokacin da ya ke shugaba. Amma daga baya an hanɓare shi aka kuma kama shi, amma dai ba a miƙa shi ga kotun ba a Hague.

An tuhumi jagoran 'yan tawaye na Lord's Resistance Army (LRA) a Uganda Joseph Kony da laifukan yaƙi da na keta haƙƙin ɗan'adam, kuma shi ne wanda ICC ta fi daɗewa tana nema.

An bayar da sammacin kama shi a 2005. A farkon shekarar nan, alƙalan kotun sun bayar da dama ga masu shigar da ƙara su gabatar da tuhume-tuhume a kansa duk da yake ba ya nan.

Duk da yake akwai gagarumin ƙalubale game da wannan lamari, Boyle, wanda ya taka rawa a Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Yugoslavia (ICTY), ya yi amannar cewa tabbatar da adalci abu ne mai yiwuwa.

"Ana daɗewa ba a yi adalci ba, amma daga ƙarshe kwalliya tana biyan kuɗin sabulu," in ji shi.

"Na soma tattara bayanai kan tuhumar Slobodan Milosevic a ICC a watan Maris na 1993. Na gabatar da ƙara game da zarginsa da aikata kisan kiyashi da laifukan yaƙi da na take haƙiƙin ɗan'adam kan ’yan ƙasar Bosnia. Daga nan na gamsar da mai shigar da ƙara na Kotun ICTY, Carla Del Ponte, domin a tuhimi Milosevic kan aikata kusan duka laifukan da kotun ta hana, ciki har da kisan kiyashi sau biyu."

Slobodan Milosevic ya mutu a kurkuku da ke ICC a 2006. Shi ne shugaban ƙasa mai ci na farko da alaka kama da laifin kisan ƙare-dangi da laifukan yaƙi da na take hakkin ɗan'adam,/Hoto: Reuters

A shekarar 2004 aka tuhumi shugaan na Serbia a Kotun da ke birnin Hague.

Boyle ya je yankin Srebrenica da ke gabashin Bosnia da kuma Herzegovina, inda aka kashe kusan mutum 8,000. Yana kallon abin da ke faruwa Gaza a matsayin irin wanda ya faru a kisan ƙare-dangi na 1995.

“An kashe Falasɗinawa 40,000. An jikka dubu tamanin, sannan an lalata kusan ɗaukacin Gaza ... don haka idan (ICC) ba ta ɗauki mataki ba, za ta kasance abar tuhuma a tarihi."

Mayar da hankali kan 'yan Afirka

Wannan ne karo na farko da kotun ICC take neman kama wani shugaba da ƙasashen Yamma suke goyon baya.

"Ana kiran Kotun ICC a matsayin kotun fararen-fata," in ji Boyle.

A shekarar 2012 lokacin da mai shigar da ƙara na farko na kotun, Luis Moreno Ocampo, ya bar ofis, ICC tana gudanar da tuhume-tuhume guda shida — dukansu a kan 'yan Afirka – abin da ya sa aka riƙa sukar kotun wadda ake gani tamkatar ta Turawa ce da ke tuhumar 'yan Afirka.

Umarnin da kotun ke neman bayarwa domin kama Netanyahu da ministan tsaronsa Gallant ya zama wani abu da zai wanke kotun daga zargin da ake yi mata na nuna son kai.

Watakila bukatar bayar da sammacin kama Netanyahu da Gallant su sauya salon kotun.

“A yau, muna sake jadda cewa dokokin duniya da dokokin yaki sun shafi kowa. Ba maganar cewa wadannan ne sojojin da ke yaki, ba maganar wannan ne kwananda, ba maganar wannan ne jagoran fararen hula – ba wani – da zai yi abin da ya ga dama kuma ya sha,” a cewar Mai Shigar da Kara Khan.

Boyle ya bayyana cewa, “abu ne mai wahala a tsayar da kisan kare dangi lokacin da ake tsaka da yinsa.” Amma yana fatan cewa samun shugabannin Isra’il da laifi zai sa rundunar sojan Isra’ila ta sake tunani kan yakin, kuma mai yiwuwa ta ba da gudunmuwa wajen tsagainta wuta nan take kuma mai dorewa a Gaza.

Baya ga yankin Gabas ta Tsakiya, akwai wasu kuma da suke so a hukunta kawayen Isra’ila, musamman masu ba ta makamai.

TRT Afrika