Global Outage at Berlin airport BER / Photo: Reuters

Masu amfani da fasahar Microsoft a faɗin duniya, ciki har da bankuna da kamfanonin jiragen sama, sun ba da rahoton cewa an samu katsewar intanet a ranar Juma'a, sa'o'i kaɗan bayan da kamfanin ya sanar da cewa ana ƙoƙarin shawo kan matsalar da ta danganci rashin samun damar amfani da manhajar Microsoft 365 da sauransu.

Babu cikakken bayani game da takamaimai abin da ya jawo katsewar ta intanet. Sai dai Microsoft ya wallafa wani saƙo a shafin X da ke cewa an soma shawo kan matsalar ko da yake mutane a faɗin duniya suna ci gaba da bayyana ƙalubalen da suke fuskanta na katsewar intanet.

Shafin intanet na DownDetector, wanda ke bin diddigin yadda ake amfani da intanet, ya ce an samu katsewar intanet a kamfanonin bayar da biza, da kamfanin samar da tsaro na ADT da Amazon, da kuma kamfanonin jiragen sama ciki har da American Airlines da Delta.

Kafafen watsa labarai a Australia sun ruwaito cewa kamfanonin jiragen sama da kamfanonin sadarwa da bankuna da kafofin watsa labarai sun fuskanci katsear intanet a kwamfutocinsu. Kazalika wasu bankuna a New Zealand sun ce sun fuskanci katsewar intanet.

Microsoft 365 ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa yana "aiki wajen samar da wasu hanyoyin samun intanet da zummar rage tasirin wannan matsala”, yana mai cewa yana ganin “lamura suna komawa daidai.”

Kamfanin bai mayar da martani ba game da buƙatar da aka yi masa ta yin ƙarin bayani. Kazalika bai yi bayani kan dalilin da ya haifar da katsewar intanet ɗin ba.

Hukumomi a Australia sun bayar da rahotannin katsewar intanet a wurare daban-daban ciki har da bankunan NAB, Commonwealth da Bendigo, kuma kuma kamfanonin jiragen sama na Virgin Australia da Qantas, tare da kamfanonin intanet da waya irin su Telstra.

Haka kuma kafofin watsa labaran Australia — cikinsu har da ABC da Sky News — sun kasa watsa labarain talbijin da rediyo sakamakon katsewar intanet.

AP