Ƙasashen Yamma irin su Amurka sun rufe idanunsu sun yi mirsisi suna goyon bayan hare-haren da Isra'ilan ke kai wa yankin, inda ake kashe fararen hula. Photo: Reuters Archive

Haɓakar ƙyamar Musulmai a Turai da Amurka ya haifar sa nuna wariya ta zama a kan gaba a shekarar 2023.

Gwamnatocin da aka kafa a matsayin ginshiƙan tabbatar da 'yanci sun kasance masu goyon bayan ƙiyayya kai tsaye ko a kaikaice kuma a wani yanayi na musamman a matsayin tabbatar da "dimokuradiyya kaɗai a Gabas ta Tsakiya."

Hare-haren da Isra'ila ke kai wa kan gidajen mutane da asibitoci da makarantu da masallatai da coci-coci a Gaza sun sa ƙasashen duniya suna ta neman a tsagaita wuta. Ana kai hare-haren ne kan Masallacin Ƙudus da wuraren masu tsarki na Falasɗinawa.

Amma an ci gaba da take hakkokin ƴan'adam a yankunan Falasɗinawa da aka mamaye tun ranar 7 ga watan Oktoba, a lokacin da ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta ƙddamar da wani harin ba-zata a kan Isra'ila.

An yi amannar har yanzu akwai mutane da dama a ƙarƙashin ɓaraguzai a Gaza, inda aka lalata kayayyakin more rayuwa da suka haɗa da asibitoci dsa makarantu da wuraren ibada a hare-haren da ake kai wa.

Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya sanar a ranar 9 ga watan Oktoba cewa zai katse lantarki da hana shigar da abinci da fetur.

A kwanakin da suka biyo baya, rundunar sojin Isra'ila ta dakatar da ayyukan jinƙai.

Tun daga 10 ga watan Oktoba, Isra'ila ta dinga kai hare-haren sama ba ƙaƙƙautawa kan gidajen mutane da asibitoci da makarantu da wuraren ibada.

Ƙasashen Yamma irin su Amurka sun rufe idanunsu sun yi mirsisi suna goyon bayan hare-haren da Isra'ilan ke kai wa yankin, inda ake kashe fararen hula.

Duk da hare-haren da dakarun da ke da alaƙa da gwamnatin Tel Aviv ke kai wa, ƙasashen yammacin duniya da suka hada da Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da Italiya sun ƙi fitar da sanarwar la'antar hare-haren Isra'ila.

Ƙona Ƙur'ani a Turai

Dan siyasar kasar Denmark Rasmus Paludan mai tsatsauran ra'ayi ya ƙona Ƙur'ani a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke Stockholm a ranar 21 ga watan Janairu da kuma ofishin jakadancinta da ke Copenhagen a ranar 27 ga watan Janairu.

Paludan ya ci ga da ƙona Ƙur'ani da nufin tsokana inda ya yi hakan a Malmo da Norrkoping da kuma Jonkoping a lokacin hutun Ista a watan Afrilu.

Salwan Momika dan asalin ƙasar Iraƙi ya kuma ƙona Ƙur'anin ƙarkƙshin kariyar ‘yan sanda a gaban Masallacin Stockholm a ranar 28 ga watan Yuni, daidai da ranar farko ta bikin Babbar Sallah.

A ranar 20 ga watan Yuli a gaban ofishin jakadancin kasar Iraki na Stockholm da kuma a ranar 31 ga watan Yuli a gaban ginin majalisar dokokin kasar Sweden, Momika ya tattaka Ƙur’ani da tutar ƙasar Iraƙi ƙarƙashin kariyar ‘yan sanda.

Bayan sanarwar da Ministan Ilimi Gabriel Attal ya bayar a ranar 27 ga watan Agusta na cewa za a haramta amfani da abaya ga mata a makarantu a kasar Faransa, kungiyar ADM mai fafutukar kare hakkin Musulmai ta kai ƙorafin hakan ga majalisar dokokin kasar.

Majalisar dokokin kasar Faransa ta yi watsi da bukatar dakatar da dokar a ranar 7 ga watan Satumba, inda ta ce ɗalibai mata na sanya abaya, ɗalibai maza kuma suna sanya rigar kamis, wata rigar gargajiya, saboda dalilai na addini.

Wani rahoto da aka buga a watan Nuwamba kan ƙyamar Musulmai a Jamus ya nuna cewa mutum daya cikin kowane mutum biyu a kasar ya amince ko ya yi amfani da kalamai na "ƙiyayya ga Musulmai."

Ministar Harkokin Cikin Gida Nancy Faeser ta sanar da cewa ƙyamar Musulmai ta taso a baya-bayan nan kuma za a ƙara inganta hanyoyi da cibiyoyin ba da shawarwari a shekara mai zuwa.

A kasar Netherlands, akalla kananan hukumomi 10 ne suka gudanar da bincike a asirce kan masallatai da limamai da shugabannin kungiyoyin addini da kuma masu faɗa a ji a wuraren ibadu.

An bayar da rahoton cewa, binciken, wanda Hukumar Tsaro da Yaki da Ta’addanci ta kasar Holland ta dauki nauyin gudanar da shi ta hanyar ƙananan hukumomi, wani kamfani mai zaman kansa mai suna NTA, Nuance door Training en Advies ne ya gudanar da binciken.

Ministan Harkokin Zamantakewa da Ƙwadago Karien van Gennip ya bayyana nadama game da binciken kuma ya ce za a koyi darasi.

Ƙin Musulmai a Amurka

Wani rahoton haƙƙin ɗan'adam da Cibiyar Kula da Dangantakar Musulmai da Amurkawa (CAIR) ta fitar a watan Afrilu ya ce ƙorafe-ƙorafen da ake samu na ƙin Musulmai da nuna musu wariya ya ragu da 202, amma ƙorafe-ƙorafen da ake samu a fannin ilimi ya ƙru da kashi 33 cikin 100.

A watan Yuni, wasu ƴan jam'iyyar Democrat a Majalisar Dokokin Amurka sun gabatar da wata doka ta yaƙi da ƙin Musulunci ta ƙasa da ƙasa, don yaƙi da ƙaruwar ƙin Musulmai da ake samu a faɗin duniya.

Wasu masu kutse a intanet ƴan ƙasar Switzerland da suka ƙwace wani jerin sunaye na Hukumar Bincike ta Amurka ranar 13 ga watan Yuni, sun kwarmata bayanan ga al'umma.

An gano cewa an bi diddigin mutum miliyan 1.5 a asirce da suka haɗa da yara ƴan shekara bakwai da masallatai 2,500, mafi yawansu masu sunayen Larabawa da Musulmai na tsawon shekara 20.

CAIR ta shigar da ƙarar gwamnati kan jerin sunayen da FBI din ta fitar na sa ido a kan ta'addanci. Ƙarar ta haɗa da manyan jami'an gwamnati 29 da hukumomi da ministoci da shugaban FBI da na Hukumar Leƙen Asiri ta Amurka ta CIA da babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, har da na gwamnatin Joe Biden.

Ƙaruwar ƙiyayya a Indiya

A yankin Gurugram da ke Jihar Haryana ta Indiya, wasu kasuwanni mallakar Musulmai da suka fuskanci ƙone-ƙone, tare da wani masallaci, da kuma kisan wani limami da kungiyoyin Hindu masu tsattsauran ra'ayi suka yi a ranar 8 ga watan Agusta, sun haifar da damuwa a tsakanin Musulmai.

Bayan hare-haren da aka kai kan wasu tsiraru, kungiyar Hindutva Watch ta bayar da rahoto a ranar 26 ga watan Satumba cewa, an kai hare-hare sama da 250 kan Musulmai a Indiya a farkon rabin shekarar 2023.

Rahoton ya yi nuni da yadda ake samun ƙaruwar kalaman ƙyama ga Musulmai tun bayan da Jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) mai kishin ƙasa ta hau kan karagar mulki a shekara ta 2014, tare da yin nuni da cewa jami'an gwamnati sun tsunduma cikin cin zarafi da kalaman ɓatanci ga musulmi da ƙimar Musulunci.

TRT World