1712 GMT — Adadin Falasdinawan da suka mutu a Gaza ya zarce 16,000
Adadin Falasdinawa da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila ya kai 16,248 tun farkon yakin Isra'ila a Gaza.
Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun ce adadin wadanda suka mutun ya hada da yara 7,112 da kuma mata 4,885.
1651 GMT — Falasdinawa 7,800 ne ke tsare a gidajen yarin Isra'ila: NGO
Fursunonin sun hada da mata 33, da kananan yara 166, da kuma mutum 2,873 da ake tsare da su ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba, ko tuhumarsu, a karkashin wata mummunar siyasar Isra’ila ta tsare tsare-tsaren gudanarwa, in ji kungiyar fursunonin Falasdinu a cikin wata sanarwa.
"Sojojin Isra'ila sun tsare Falasdinawa 3,580 a Yammacin Kogin Jordan tun ranar 7 ga watan Oktoba," in ji kungiyar.
1349 GMT — Isra'ila ta kai hare-hare da makaman atilare fiye da 100,000 Zirin Gaza
Isra'ila ta kai hare-hare da makaman atilare sau fiye da 100,000 Zirin Gaza tun daga ranar 27 ga watan Oktoban da ya wuce zuwa yanzu.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce "An harba makaman atilare sama da 100,000 tun lokacin da aka fara kai hare-hare ta ƙasa."
Ya jaddada cewa makamin atilare "na taka muhimmiyar rawa a cikin yaƙin yayin da suke ba da babbar kariya ga sojojin da ke taka rawa a fagen daga a Gaza.
Rundunar ta ce dakarunta na ƙasa suna gudanar da ayyukan soji a yankin Jabalia da ke arewacin Gaza.
1414 GMT — Sojojin Isra'ila 80 ne suka mutu a yakin kasar da Gaza
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe sojojinta 80 tun bayan fara kai farmakin da suke kai wa Gaza.
Bayan shafe makwanni ana kai hare-hare masu tsanani, Isra'ila ta kai farmaki ta ƙasa a yankin a ranar 27 ga watan Oktoba.
1234 GMT — Isra'ila ta yi amfani da makaman da Amurka ta kera wajen kashe fararen hula 43 a Gaza: Amnesty International
Rundunar sojin Isra'ila ta kashe Falasdinawa 43 ta hanyar amfani da makamin da Amurka ta ƙera a wasu bayanan da aka rubuta kan wasu hare-haren sama biyu da aka kai yankin Gaza da aka killace, in ji ƙungiyar Amnesty International.
"Wani sabon bincike da Amnesty International ta gudanar ya gano cewa sojojin Isra'ila sun yi amfani da makaman da Amurka ta ƙera a hare-haren wuce gona da iri da suka kai kan gidajen da ke cike da fararen hula a Zirin Gaza," kamar yadda ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X.
Kungiyar ta ƙara da cewa "Hare-haren biyu sun kashe jimillar fararen hula 43. A duka biyun, wadanda suka tsira da rayukansu sun ce babu wani gargadi da aka yoi kafin kai harin."
"Wadannan hare-haren ko dai hare-hare ne kai tsaye kan fararen hula ko kuma hare-haren wuce gona da iri. Dole ne a bincike su a matsayin laifukan yaƙi," in ji Amnesty.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Amurka da ta dakatar da bai wa Isra'ila makamai.
1101 GMT — Halin da ake ciki a Gaza yana ƙara muni duk bayan sa'a daya
Wani jami'in hukumar Lafiya ta Duniya a Gaza ya ce halin da ake ciki a yankin yana taɓarɓarewa duk bayan awa ɗaya, sakamakon hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kudancin yankin kusa da biranen Khan Younis da Rahaf.
"Halin da ake ciki a yana taɓarɓarewa duk sa'a guda," kamar yadda Richard Peeperkorn, WHO a yankin na Falasɗinu da aka mamaye ya shaida wa manema labarai.
"Ana ci gaba da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa ta ko ina, ciki har da nan a yankunan kudanci, Khan Younis da ma a Rafah."
Jami'in ya kuma lura cewa hukumar lafiya ta damu matuƙa game da raunin tsarin kiwon lafiya a kudancin Gaza.
A matsakaicin ƙiyasi ana kashe yaro daya a kowane minti 10 a Gaza, in ji wakilin, yana mai kiran lamarin "lokaci mafi duhu ga bil'adama."
1040 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 50 a biranen Khan Younis da Deir al- Belah da ke Falasdinu
Akalla Falasdinawa 50 Isra’ila ta kashe a biranen Khan Younis da ke kudancin Falasdinu da kuma Deir al-Belah da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda aka kiyasta.
Kamfanin dillancin labarai na Falasdinu wato WAFA ya bayar da rahoton wannan harin wanda ya ce ya rutsa da farar hula da dama.
A Khan Younis kadai, Falasdinawa 40 Isra’ilar ta kashe sannan ta kashe wasu goma a Deir al-Belah.
0455 GMT — Hotunan tauraron dan'adam sun nuna yadda Isra'ila ta soma kai hari ta kasa a kudancin Gaza
Hotunan tauraron dan'adam da kamfanin dillancin labarai na The Associated Press ya yi nazarinsu sun nuna yadda dakarun Isra'ila suka soma kai hari ta kasa a kudancin Gaza.
Hotunan tauraron dan'adam din da kamfanin Planet ya dauka sun nuna girma da kuma kaifin yakin da Isra'ila take yi.
Kamfanin na Planet Labs PBC ya dauki hotunan ranar Lahadi, inda suka nuna tankokin yakin Isra'ila a wani wuri mai nisan kasa da kilomita 6 daga arewacin tsakiyar Khan Younis, babban birni da ke kudancin Gaza.
Yanzu haka mutanen da suka tsere daga hare-hare ta sama da Isra'ila ke kaiwa a Birnin Gaza da ke arewacin yankin suna zaune a Khan Younis da yankunan da ke kewayensa bayan sojojin Isra'ila sun umarci su bar gidajensu.
0038 GMT — Isra'ila na duba yiwuwar sakar ruwa cikin gine-ginen karkashin kasa da ke Gaza — WSJ
Isra'ila ta tattara wasu manya-manyan bututai da za su malala ruwa cikin gine-ginen karkashin kasa da kungiyar Hamas take amfani da su a Gaza da aka mamaye a yunkurin fatattakarsu daga ciki, kamar yadda jaridarWall Street Journal ta Amurka ta rawaito, inda ta ambato wasu jami'an gwamnatin kasar.
A tsakiyar watan Nuwamba, rundunar sojin Isra'ila ta gama kafa manyan bututai akalla biyar a wani wuri mai nisan kusan mil daya daga arewacin sansanin 'yan gudun hijira na Al Shati wadanda za su iya sheka ruwa da yawansa zai kai dubban kyubik mita cikin awa daya, domin mamaye dukkan gine-ginen karkashin kasar cikin makonni kadan, in ji rahoton.
Babu cikakken bayani kan ko Isra'ila za ta malala ruwan kafin a saki dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, a cewar labarin. A baya Hamas ta ce ta ajiye dukkan mutanen da ta yi garkuwa da su a "wurare masu aminci da kuma gine-ginen karkashin kasa."
A lokacin da aka yi masa tambaya game da wannan batu, wani jami'in gwamnatin Amurka ya ce yana da kyau Isra'ila ta lalata gine-ginen karkashin kasar kuma kasar tana duba hanyoyi daban-daban na yin hakan.
Jaridar Wall Street Journal ta ce wani jami'in Rundunar Tsaron Isra'ila ta Defense Forces [IDF] ya ki cewa uffan kan wannan shiri ko da yake ta ambato shi yana cewa: "Rundunar IDF tana yin aiki domin kawar da ta'addancin Hamas ta hanyoyi daban-daban, inda take amfani da karfin soji da kuma fasahohi."
0123 GMT — Kungiyar bayar da agaji ta Palestine Red Crescent ta daina jin duriyar ma'aikatanta da ke Gaza
Kungiyar bayar da agaji ta Palestine Red Crescent Society ta ce ta daina jin duriyar tawagar likitocinta da ke yankin Gaza da aka mamaye.
Ta bayyana haka ne bayan kamfanin sadarwa na Palestine Telecommunications Company [PalTel] ya ce an katse dukkan sadarwa da intanet a Gaza.
"Mun daina jin duriyar ma'aikatanmu da ke Zirin Gaza sakamakon matakin da Isra'ila ta dauka na katse dukkan kamfanonin sadarwa," in ji wata sanarwa da Red Crescent ta fitar.
Ta bayyana matukar damuwarta game da rashin tsaron da tawagarta ke ciki a Gaza sakamakon luguden wutar da jiragen yakin Isra'ila suke yi a yankin.
Kungiyar ta ce katse hanyoyin sadarwar zai shafi masu kai agajin gaggawa a wuraren da aka yi wa luguden wuta a Gaza da kuma zai hana mutanen da ke neman agajin gaggawa kiran layin waya na gaggawa mai lamba 101 domin nean dauki.
0109 GMT — Dakarun Isra'ila sun kashe Falasdinawa 2 a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan
Dakarun Isra'ila sun kashe Falasdinawa biyu a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
Anas al Farroukh, mai shekara 23, da Mohammad al Farroukh, mai shekara 22, dukkansu sun samu munanan raunuka kafin a bayyana cewa sun mutu a asibiti, kamar yadda wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA, yana mai ambato Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu.
WAFA ya kara da cewa lamarin ya faru ne a yankin Ras Al Aroud a garin Sa'ir a arewa maso yammacin Hebron.