1736 GMT — Sojojin Isra'ila suna aiki 'tsakiyar birnin Gaza — minista
Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce sojojin Isra'ila suna aiki a "tsakiyar birnin Gaza."
A wani taron manema labarai da aka watsa ta gidan talbijin, Gallant ya ce daga Isra'ila har Hamas ɗin ba za su iya mulkar yankin Falasdinu ba da zarar an kawo karshen rikicin da ake yi.
Ana ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa tsakanin ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa da dakarun Isra'ila, a cewar rahotannin dake fitowa daga filin daga.
1440 GMT — Isra'ila ta kawo cikas ga sakin ƴan ƙasashen waje da ake garkuwa da su a Gaza — Hamas
Hamas ta ce Isra'ila ta kawo cikas wajen sakin wasu 'yan kasashen waje 12 da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawan ke garkuwa da su a Gaza.
"Mun tsara yadda za a saki mutanen 12 da aka yi garkuwa da su, wadanda ‘yan kasashen waje ne, a cikin kwanakin da suka gabata, amma mamayar da Isra’ila ke yi ta kawo cikas ga yunƙurin,” in ji reshen kungiyar ta Qassam Brigades a cikin wata sanarwa.
"A shirye muke mu sake su, amma halin da ake ciki a yanzu da kuma hare-haren Isra'ila sun hana faruwar hakan," in ji Hamas.
1509 GMT — Faransa ta ce ta kwashe ƴan ƙasarta fiye da 100 daga Gaza
Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da cewa, an kwashe sama da 'yan kasarta 100 da iyalansu da su daga Gaza ta kan iyakar Rafah zuwa Masar.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce wasu tawagogi biyu na Faransawa da jami'ai sun samu damar ficewa a ranakun Litinin da Talata daga Gaza kuma suna nan lafiya a Masar.
Kwashe su din "ya kawo adadin wadanda akwa kwashe karkashin shirin Faransa zuwa sama da mutum 100," in ji sanarwar.
1351 GMT — Isra'ila ta kai hari gidajen mutane a wata unguwa a Gaza
Aa fargabar mutuwar mutane da dama a wani sabon harn sama da Isra'ila ta kai kan gidajen mutane a unguwar Deir al Balah da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda wani jami'in Falasɗinu ya saida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
1340 GMT — Ana kashe yara 160 a Gaza a kullum: WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya a ranar Talata ta ce kusan yara 160 ake kashewa a duk rana a Gaza a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa.
Zuwa yanzu, akalla Falasdinawa 10,328 aka kashe, daga ciki har da yara 4,237 da kuma mata 2,719.
Sama da mutum 25,956 aka raunata sakamakon hare-haren Isra’ila.
0940 GMT — Hare-haren Isra'ila sun tilasta wa kashi 70 na mutanen Gaza barin muhallansu
Hukumomi a Gaza sun ce kashi 70 cikin 100 na al'ummar yankin "an tilasta musu barin gidajensu" saboda hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai musu.
Kiyasi ya nuna cewa al'ummar Gaza sun kai mutum miliyan 2.3.
A wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar a ranar Talata ya ce, hare-haren Isra'ila sun lalata kashi 50 cikin 100 na gidajen da ke fadin Gaza, kuma kashi 10 cikin 100 na gidajen an lalata su baki daya ko kuma ba za a iya zama a cikinsu ba.
Kazalika sanarrwar ta ce rabin asibitoci da kashi 62 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya a Gaza ba sa aiki.
0800 GMT — Israila za ta kwace ikon wanzar da tsaro a Gaza bayan yaki: Netanyahu
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce kasarsa za ta "kwace ikon wanzar da tsaro" a Gaza har sai abin da hali ya yi idan ta kammala yaki da kungiyar Hamas.
"Isra'ila za ta dauki alhakin tabbatar da tsaro har sai abin da hali ya yi," in ji shi a hirar da ya yi da kafar watsa labarai ta ABC News.
"Idan ba mu dauki nauyin tabbatar da tsaro ba, za mu fuskanci barkewar ta'addanci daga kungiyar Hamas irin wanda ba mu taba tsammani ba," a cewarsa.
0730 GMT — Isra'ila ta rusa masallatai 56 a Gaza
Isra'ila ta lalata masallatai 192, cikin har da 56 da ta lalata baki daya tun da ta soma kai gari a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar Ofishin Watsa Labarai na Gaza a sanarwar da ya fitar Litinin da maraice.
"Hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gaza sun lalata masallatai 192, ciki har da 56 da ta rusa baki daya, baya ga coci uku da ta rusa,” a cewar mai magana da yawun ofishin na Watsa Labarai Salama Marouf a taron manema labarai da ya gudanar a Birnin Gaza.
Ya kara da cewa hare-haren sun rusa cibiyoyin kiwo lafiya 192 da kuma motocin daukar marasa lafiya 32 kana sun lalata cibiyoyin kiwon lafiya 113, yayin da asibitoci 16 da cibiyoyin samar da lafiya 32 suka daina aiki.