Qatar ta ce nan da kwanaki hudu za a sako mutane 50 da aka yi garkuwa da su. / Photo: Reuters

1430 GMT — Qatar mai shiga tsakani ta ce yarjejeniyar Isra'ila da Hamas za ta fara aiki da ƙarfe 7 na safiyar Juma'a

Za a dakatar da kai hare-hare a Gaza da karfe 7 na safe agogon GMT a ranar Juma'a, in ji Qatar.

"Za a yi musayar rukunin farko na farar hula da aka yi garkuwa da su da misalin karfe 4 na yammacin ranar Juma'a," in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Majed Al Ansari a wani taron manema labarai a Doha.

Ya ce nan da kwanaki hudu za a sako mutane 50 da aka yi garkuwa da su.

Rukunin farko na wadanda aka yi garkuwa da su za su hada da mata da yara 13,” ya ƙara da cewa.

1225 GMT — Sojojin Isra'ila sun tsananta kai hare-hare ta sama a Gaza gabanin tsagaita wuta

Sojojin Isra'ila sun sanar da cewa sun kai hare-hare ta sama kan wurare 300 a Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata, daidai lokacin da ake sa ran dakatar da ayyukan jinƙai na ɗan lokaci a cikin sa'o'i masu zuwa.

A wata sanarwa, rundunar sojin ta ce ta kai hare-haren ne da nufin samun "wuraren da ke da alaƙa da Hamas," wato ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa a yankin da aka yi wa ƙawanya, kuma an kai hare-haren ne "ta sama."

Ta ce wuraren sun haɗa da "hedkwatar da ƙungiyar ke gudanar da ayyukanta, da gine-ginen ƙarƙashin ƙasa, da wuraren ajiyar kayayakin soji da makamai," a cewar sanarwar sojin.

Babban hafsan rundunar sojin Isra'ila Herzi Halevi ya shaida wa shugabannin sojojin da ke cikin Gaza a ranar Alhamis cewa, "ba za mu dakatar da yaƙin ba, a maimakon haka, za mu ci gaba har sai an samu nasara da kuma ci gaba," a cewar sanarwar.

Ba za a iya tabbatar da ikirarin na Isra'ila ba kai tsaye. Hamas na yawan cewa Isra'ila na kai hare-hare ne kan fararen hula da gayya.

Fararen hula Falasdinawa suna shan wahalar yaƙin da Isra'ila ta kwashe makwanni tana yi na soji, inda Isra'ila ke jefa bama-bamai a Gaza, da kai hari kan makarantu da masallatai da asibitoci.

Ba za a iya tabbatar da ikirarin na Isra'ila ba kai tsaye. Hamas na yawan cewa Isra'ila na kai hare-hare ne kan fararen hula da gayya. . / Photo: Reuters

Ofishin yada labarai na yankin da aka yi wa ƙawanya ya ce adadin mutanen da aka kashe a hare-haren sama da na ƙasa a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai fiye da 14,000, da suka haɗa da yara da mata.

0831 GMT — Sojojin Isra'ila sun bukaci mutane su fita daga Asibitin Indonesia da ke Gaza cikin awa 4

Sojojin Isra'ila sun bukaci mutane su fita daga Asitibin Indonesia da ke Arewacin Gaza cikin awa hudu, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Faladinu.

Sojojin na Isra'ila suna so su shiga asibitin domin "gudanar da wani aikin soji" kuma sun nemi a kwashe kowa daga cikinsa nan da awa hudu, in ji Darakta Janar na Ma'aikatar Lafiya Dr Munir Al Borsha hira da Al Jazeera.

Al Borsh ya ce sojojin Isra'ila sun yi wa Asibitin Indonesia kawanya kuma suna ci gaba da kai hare-hare a kewayensa.

Ya ce akwai marasa lafiya 200 a asibitin, yana mai cewa tuni masu larura 450 suka fita daga cikinsa ranar Laraba.

Al Borsh ya kara da cewa akwai gawa 65 da ba za a iya binne su ba, inda ya kara da cewa 50 daga cikinsu sun kwashe fiye da kwana 10 a lambun da ke asibitin.

0727 GMT — Ministan Isra'ila ya yi barazanar yin murabus idan aka daina kai hari a Gaza

Ministan Tsaron Isra'ila mai ra'ayin rikau, Itamar Ben-Gvir ya yi barazanar yin murabus daga gwamnatin kasar idan aka kawo karshen hare-haren da kasar ke kaiwa a Gaza bayan Firaiminista Benjamin Netanyahu ya sanarwar da tsagaita wuta ta kwanaki hudu don kai kayayyakin jinkai.

Ben-Gvir ya bayyana haka ne ta gidan talabijin na Channel 14, inda ya yi tsokaci kan amincewar gwamnatin Isra'ila game da kai kayan jinkai yankin Falasdinu.

Ben ya yi fatali da matakin.

Ya ce ya ji daga bakin Netanyahu cewa za a sake komawa bakin daga bayan tsagaita wuta na kwanaki hudu, amma idan har ba a ci gaba da kai hare-hare ba, ‘’to tabbas babu ruwanmu da wannan gwamnati."

Dakarun Isra'ila suna sintiri a kewayen Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza. / Hoto: Reuters

0651 GMT — Dakarun Isra'ila sun kama daraktan Asibitin Al Shifa da ma'aikata da dama

Wani likita a Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza ya ce dakarun Isra'ila sun kama daraktan asibitin da wasu ma'aikatansa.

"An kama Dakta Mohammad Abu Salmiya tare da manyan likitoci da dama," a cewar Khalid Abu Samra, shugaban bangarori na asibitin wanda yake tsaka da ce-ce-ku-ce a game da hare-haren da suka kaiwa a yankin.

Isra'ila ta kashe Falasdinawa 14,532 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, daga cikinsu akwai mata fiye da 6,000 da kananan yara 4,000, a cewar hukumomin Falasdinu. /Hoto: Reuters

0422 GMT — Isra'ila ta kara kaimi wurin kai hare-hare a Gaza gabanin lokacin tsagaita wuta

Isra'ila ta kara kaimi wurin kai hare-hare a fadin Gaza gabanin lokacin tsagaita wuta da aka amince da shi tsakanin dakarunta da masu fafutuka na kungiyar Hamas ya soma aiki.

Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare a yankuna da dama na yankin da aka mamaye, musamman a arewacin Gaza, kamar yadda kafanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA ya rawaito.

Ya kara da cewa an kashe mutane da dama sakamakon hare-haren na sojojin Isra'ila a wasu gidaje da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat.

0334 GMT — Amurka ta kama wasu jiragen yaki marasa matuka da aka harba daga Yemen: Pentagon

Amurka ta kama wasu jiragen sama marasa matuka da aka harba daga yankunan da ke karkashin ikon Houthi a Yamen, in ji rundunar tsakiya, CENTCOM.

An harbo jiragen ne a lokacin da jirgin yakin Amurka ke sintiri a Tekun Maliya. Jirgin da ma'aikatan jirgin ba su lalace ko jin rauni ba, "in ji CENTCOM a shafin X.

0307 GMT — Biden ya ce Amurka ba za ta bari a tursasa wa Falasdinawa fita daga Gaza ba

Shugaban Amurka Joe Biden ya shaida wa takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi ta wayar tarho cewa kasarsa ba za ta amince a tursasa wa Falasdinawa fita daga yankin Gaza da aka mamaye ba, ko kuma Gabar Yammacin Kogin Jirdan, kamar yadda wata sanarwa daga Fadar White House ta bayyana.

"Shugaban kasa yana mai tabbatar da shirinsa na kafa kasar Falasdinawa da kuma jaddada muhimmancin rawar da Masar za ta taka wajen ganin an bi wadannan ka'idoji," in ji White House.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Biden ya bayyana jin dadinsa "game da kokarin Masar na kulla yarjejeniyar sakin mutanen da Hamas ta kama tare da tsagaita wuta a Gaza."

Wasu yara Falastinawa kenan aka kawo su asibitin Shifa wadanda suka jikkata a harin da isra'ila ta kai Gaza ranar 11 ga Oktoban 2023./ Hoto: AP

2205 GMT — Isra'ila ta 'kashe' ɗan babban dan majalisar Hezbollah

An kashe ɗan wani babban dan majalisar dokokin Hezbollah a wani harin da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon, kamar yadda wata majiya ta kusa da danginsa ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.

Majiyar wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce, "Abbas Raad, ɗan shugaban majalisar dokokin kungiyar Hezbollah Mohammed Raad, "an kashe shi ne tare da wasu 'yan kungiyar Hezbollah " a wani harin da Isra'ila ta kai a wani gida a Beit Yahun.

Kamfanin dillancin labarai na Labanon ya rawaito cewa, "wani hari ta sama da maƙiya Isra’ila suka kaddamar kan wani gida a Beit Yahun, ya kashe mutane hudu tare da jikkata wasu daban.

Daga bisani kungiyar Hezbollah ta ce harin da Isra'ila ta kai kan wani gida a kauyen Yahun ya kashe mayakanta biyar ciki har da dan babban dan majalisar dokokin Hezbollah.

TRT Afrika da abokan hulda