1357 GMT –– Jiragen saman Masar suna jefa abinci kayan agaji a tsakiyar yankin arewacin Gaza
Sojojin saman Masar sun yi wani aiki na jefa kayan agajin jinƙai a Gaza, kamar yadda kafafen yada labaran ƙasar suka bayyana.
Kafar watsa labaran ta Al Qahera ta ce, an gudanar da jefa kayan daga jiragen tare da hadin gwiwar kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). Ta ce an jefa kayan agaji tan 10 a arewacin Gaza.
"An jeho wasu tan 45 na agajin jinƙai na Masar a arewaci da tsakiyar Gaza, tare da haɗin gwiwar Hadaddiyar Daular Larabawa da Jordan."
Masar ta ƙara ƙaimi ta sama da ƙasa don taimaka wa yankunan da rikicin ya shafa a arewacin Zirin Gaza tare da samar musu da agajin gaggawa," in ji Al Qahera News.
Ta ce Masar na shirin jefa ƙarin tan 50 na agajin gaggawa a arewaci da tsakiyar Gaza, ba tare da bayar da karin bayani ba.
1230 GMT — Saudiyya ta musanta rahotannin cewa ministanta ya gana da jami'in Isra'ila
Saudiyya ta musanta rahotannin da ke cewa Ministan Kasuwancinta Majid bin Abdullah Al-Qasabi ya gana da wani jami'in Isra'ila.
Kamfanin dillancin labarai na SPA ya ambato wani jami'in Saudiyya da ba a ambaci sunansa ba a ranar Litinin yana cewa ministan na Isra'ila ya gabatar da kansa ga Al-Qasabi a lokacin da yake tsaye tare da takwaransa na Nijeriya a wajen bikin buɗe Taron Ministoci na Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, a birnin Abu Dhabi, ba tare da Al-Qasabi ya san ko waye wanda ya je ya gaisa da shi ɗin ba.
Jami'in da ba a ambaci sunan nasa ba ya jaddada matsayar Saudiyya a kan batun Isra'ila da kuma jajircewarta wajen goyon bayan al'ummar Falasɗinu daga muguntar da Isra'ila ke musu, a cewar rahoton SPA.
Tun da fari a jiya Litinin, kafar watsa labaran Isra'ila, da suka haɗa da gidan talabijin na KAN, ya ce Ministan Tattalin Arziki da Ma'aikatu Nir Barkat ya gana da Al-Qasabi a wasu ƙananan taruka da aka yi a babban taron WTO a Abu Dhabi.
Babu wata alaƙar diflomasiyya tsakanin Isra'ila da Saudiyya.
0831 GMT — Amurka ta ce akwai yiwuwar Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare Gaza a lokacin azumin Ramadana
Shugaba Joe Biden ya ce Isra'ila za ta amince ta dakatar da yakin da take yi a zirin Gaza a lokacin azumin watan Ramadana mai zuwa idan har aka cimma matsaya na sako wasu daga cikin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.
Masu shiga tsakani daga kasashen Amurka da Masar da kuma Qatar na aiki kan wani shiri na yarjejeniya wadda a ƙarƙashinta ake sa Hamas za ta saki fursunonin yaƙi da dama da ta yi garkuwa da su, inda ita kuma Isra’ila ta sako fursunonin Falasɗinawa da kuma tsagaita wuta tsawon makonni shida.
A lokacin tsagaita wutar ta wucin-gadi, za a ci gaba da tattaunawa kan sakin sauran wadanda aka yi garkuwa da su.
0212 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 3 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da ta'azzara
Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu na WAFA ya rawaito cewa sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa uku a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye.
An kashe mutanen ne a harin da aka kai a garin Tubas da kuma sansanin Al-Far’a da ke kusa da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, in ji sanarwar.
Aƙalla Falasɗinawa 400 ne sojojin Isra'ila da wasu Yahudawa ƴan kaka-gida suka kashe tun ranar 7 ga watan Oktoba.
2300 GMT — Biden ya ce ana dab da tsagaita wuta a Gaza yayin da Isra'ila ke shirin mamaye Rafah
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana fatan tsagaita wuta a Gaza da aka yi wa ƙawanya ka iya fara aiki a farkon mako mai zuwa.
Da ya ziyarci birnin New York, an tambayi Biden lokacin da tsagaita wuta a yankin Falasdinawa da aka killace zai iya farawa, ya kuma amsa da cewa, "Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa ya gaya mini cewa muna kusa, mun kusa, ba mu gama ba tukuna. Fatana shi ne nan da Litinin mai zuwa za a tsagaita wuta."