Kasashen Rwanda da Chadi da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo [DRC] sun musanta kulla yarjejeniya da Isra'ila domin bai wa Falasdinawan Gaza matsuguni idan Isra'ila ta kore su daga yankinsu.
Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Rwanda ta fitar ta ce "rahotannin" da kafafen watsa labaran Isra'ila suka wallafa cewa an tattauna tsakanin kasarsu da Rwanda game da yiwuwar bai wa Falasdinawa daga Gaza matsuguni a Rwanda "karya ce tsagwaronta."
"Babu wata tattaunawa makamanciyar wannan da ta faru a yanzu da kuma a baya, kuma ya kamata a yi watsi da wannan labarin na kanzon kurege," in ji Ma'aikatar.
Tun da farko, su ma kasashen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Chadi sun musanta tattaunawa da Isra'ila domin bai wa Falasdinawa matsuguni.
Ba kamar yadda kafafen watsa labarai suke rawaitowa ba, "ba a taba yin wata tattaunawa ko shiri" tsakanin Kinshasa da Isra'ila game da zargin korar Falasdinawa tare da tsugunar da su a Kongo ba, a cewar kakakin gwamnatin kasar Patrick Muyaya a sanarwar da ya fitar ranar Alhamis da maraice.
A baya bayan nan, kafofin watsa labaran Isra'ila sun yi ta watsa rahotanni da ke cewa kasashen na Afirka guda uku za su karbi Falasdinawan Gaza, wadanda Isra'ila ta kwashe fiye da wata uku tana yi wa luguden wuta ta sama da ta kasa da kuma ta ruwa.
Hare-haren sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,600 da jikkata mutum 57,910 sannan an raba kusan mutum miliyan 2.3 da ke Gaza da gidajensu.
Wasu daga cikin ministoci masu fada-a-ji a gwamnatin Firaiminista Benjamin Netanyahu da ke da tsattauran ra'ayi suna ta kiraye-kiraye a kori Falasdinawa daga Gaza, sannan Yahudawa su sake mamaye daukacin yankin.
Kwanakin baya kafofin watsa labaran Isra'ila sun ambato wata majiya daga Ofishin Gwamnati tana cewa gwamnatin-hadakar da Netanyahu ke jagoranta tana duba yiwuwar tura dubban FalasdinawaGaza zuwa Rwanda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.