Isra'ila na matsa wa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) da ta jinkirta bayar da sammacin kame Firaminista Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaro Yoav Gallant kan laifukan yaƙi a Gaza, a cewar kafar yada labaran Isra'ila.
Majiyoyin hukuma sun ce Tel Aviv na matsin lamba na diflomasiyya kan kotun da ke Hague don jinkirta sammacin kama mutanen biyu.
"Yana da wuya a iya hasashen yadda wadannan matakan za su yi tasiri ga hukuncin alkalan," in ji jaridar Haaretz a ranar Laraba.
A ranar 20 ga watan Mayu mai shigar da ƙara na kotun ICC, Karim Khan, ya ce ya buƙaci sammacin kama Netanyahu da Gallant kan laifukan cin zarafin bil adama da laifukan yaƙi a Gaza.
Yayin da Isra'ila ta yi Allah wadai tare da yin watsi da buƙatar mai gabatar da ƙara, har yanzu babu tabbas kan yadda Tel Aviv za ta mayar da martani idan aka bayar da sammacin kama shi.
A cewar Haaretz, jami'an Isra'ila a yanzu sun shagaltu da tantance ko kotun ta ICC na da hurumin yanke hukunci kan batutuwan da suka shafi rikicin Falasdinu da Isra'ila.
Yanzu haka dai kwamitin alkalan kotun ICC na nazarin bukatar sammacin da Khan ya gabatar, wanda zai bukaci yanke hukunci kan lamarin.
Rashin amincewa da kotun
Kafin yanke hukunci, alkalan za su sake duba ra'ayoyin shari'a da kasashe da dama da kungiyoyin kasa da kasa suka gabatar game da sammacin da aka nema.
"Duk da haka, jami'an Isra'ila ba su san tsawon lokacin da wannan aikin bitar zai dauka ba," in ji Haaretz.
Isra'ila ba mamba ce a kotun ta ICC, yayin da Falasdinu ta amince da zama mamba a 2015.
Kotun ta ICC, wadda aka kafa a shekara ta 2002, kungiya ce ta kasa da kasa mai zaman kanta wadda ba ta da alaka da Majalisar Dinkin Duniya ko wata cibiya ta kasa da kasa, kuma hukunce-hukuncenta na da nasaba.
Duk da yadda Isra'ila ta yi watsi da hurumin kotun ta ICC, kotun ta shafi yankunan Falasdinawa da ta mamaye tun shekara ta 1967, inda ta ba ta damar gurfanar da jami'an Isra'ila da ake zargi da aikata laifuka a wadannan yankuna.
A wata hira da CNN a ranar 21 ga Mayu, mai gabatar da ƙara na ICC Khan ya bayyana cewa an yi masa barazana yayin da yake binciken jami'an Isra'ila.
Jami’an Isra’ila na yanzu da na baya sun yi watsi da matakin Khan, saboda rashin amincewa da hurumin kotun. Sun zargi kotun ta ICC da ƙyamar Yahudawa tare da yin kira ga ƙawayen Tel Aviv da su janye kudade tare da rusa kotun.