1158 GMT — Isra'ila ta fara kai hare-hare ta sama a Lebanon — sojoji
Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragen yaƙinta sun fara kai wasu hare-hare a kasar Lebanon, lamarin da ke ƙara nuna fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin kasashen biyu bayan shafe tsawon watanni ana luguden wuta a kan iyakokin kasar.
Sojojin kasar ba su bayar da wani ƙarin bayani kan hare-haren ta sama ba, yayin da kafafen yada labaran kasar Labanon suka rawaito cewa an kai hari a ƙauyuka uku.
Harin dai ya zo ne sa'o'i bayan da wata gobara daga Lebanon ta raunata mutane da dama a arewacin Isra'ila, a cewar likitoci.
1213 GMT — Wani jami'in Falasdinu yana da 'kyakkyawan fata' game da hukuncin da ICJ ta yanke kan mamayar Isra'ila
Wani jami'in Falasdinu ya bayyana kyakkyawan fata game da shawarar da kotun kasa da kasa (ICJ) ta bayar na goyon bayan Falasdinu dangane da yanayin mamayar Isra'ila.
Omar Awadallah, babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ya ce "Ayyukan ICJ sun yi daidai da dokokin kasa da kasa."
Ya kara da cewa "Hukuncin da kotun ta ICJ za ta yanke zai ba mu wasu sabbin iko da za mu dora wa jihohi alhakin ayyukan Isra'ila."