Hotunan zanga-zangar kasashen duniya kan kisan kiyashin da Isra'ila ta yi a asibitin Gaza

Hotunan zanga-zangar kasashen duniya kan kisan kiyashin da Isra'ila ta yi a asibitin Gaza

Al'ummar duniya sun yi matukar fusata da harin da Isra'ila ta kai a asibitin Al Ahli da ke Gaza inda ta kashe Falasdinawa akalla 500.
 Daruruwan mutane ne suka taru a gaban karamin Ofishin jakadancin Isra'ila a Istanbul domin nuna adawa da harin jiragen yakin Isra'ila suka kai asibitin Al-Ahli Baptist da ke Gaza a ranar Talata yayin da hare-haren da Isra'ila ke kai wa yankin ya shiga kwanaki 11/Hoto: AA  

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa kan mummunan harin da Isra’ila ta kai asibitin Al Ahli na Larabawa da ke Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 500 lamarin da ya fusata al'umma da dama a yankin Gabas ta tsakiya da ma sauran kasashen duniya.

Jami'an tsaron Falasdinu sun harba barkonon tsohuwa da gurneti domin tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Ramallah da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan sakamakon jifa da duwatsu da kuma rera wakokin nuna adawa da mutane ke yi kan Shugaba Mahmoud Abbas.

Masu zanga-zangar na neman Abbas ya yi murabus tare da kawo karshen hadin gwiwar gwamnatin Falasdinawa da Isra'ila a gabar Yammacin Kogin Jordan da aka wa mamaye.

Kazalika an gudanar da irin wannan zanga-zangar a kasar Turkiyya da Iraki da Jordan da Iran da Lebanon da Tunisia da Sifaniya da Amurka da sauran wasu kasashen duniya.

Falasdinawa sun yi zanga-zangar bayan da aka kashe daruruwan al'ummarsu a wani harin da aka kai a asibitin Al Ahli da ke Gaza./ Hoto: Reuters

Falasdinawa sun bi sahu sauran kasashen duniya wajen gudanar da zanga-zanga a yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye bayan harin bama-bamai da ya kashe daruruwan Falasdinawa a asibitin Al Ahli da ke Gaza.

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a wajen karamin ofishin jakadancin Isra'ila da ke Istanbul bayan mummunan harin da Tel Aviv ta kai kan asibitin Al Ahli da ke Gaza./ Hoto: AFP

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a wajen karamin ofishin jakadancin Isra'ila da ke Istanbul bayan mummunan harin da Tel Aviv ta kai kan asibitin Al Ahli da ke Gaza.

'Yan Iraqi sun shiga zanga-zanga a Bagadaza / Hoto: Reuters

'Yan Iraki sun gudanar da zanga-zanga a Bagadaza babban birnin kasar, bayan harin da aka kai kan Falasdinawa.

Al'ummar Iran sun yi zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Birtaniya da ke Tehran babban birnin kasar,/ Hoto: AFP

Al'ummar Iran sun yi zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Birtaniya da ke Tehran babban birnin kasar, don nuna goyon bayansu ga Falasdinu sakamakon harin Isra'ila akan su.

Al'ummar kasar Jordan sun gudanar da zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Isra'ila da ke Amman babban birnin kasar./ Hoto: AFP

Al'ummar kasar Jordan sun gudanar da zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Isra'ila da ke Amman babban birnin kasar, bayan mummunan harin da aka kai a asibitin Gaza.

Rahotanni sun ce wasu masu zanga-zangar sun yi kokarin kutsawa cikin ofishin jakadancin da karfi amma jami’an tsaro sun tarwatsa su.

'Yan kasar Lebanon sun gudanar da zanga-zanga tare da yin addu'o'i ga Falasdinawa a Beirut babban birnin kasar, bayan mummunan harin da Isra'ila ta kai a asibitin Al Ahli./ Hoto: Reuters

'Yan kasar Lebanon sun gudanar da zanga-zanga tare da yin addu'o'i ga Falasdinawa a Beirut babban birnin kasar, bayan mummunan harin da Isra'ila ta kai kan asibitin Al Ahli.

Al'ummar Tunisiya sun yi zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Faransa da ke Tunis babban birnin kasar, domin yin tir da harin da Isra'ila ta kai kan asibitin./ Hoto: AFP

Al'ummar kasar Tunisiya sun yi zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Faransa da ke Tunis babban birnin kasar, domin yin tir da harin da Isra'ila ta kai a asibitin Gaza.

People gather in front of the Ministry of Foreign Affairs building to protest against Israeli air strike on Al-Ahli Baptist Hospital in Gaza, in Madrid, Spain.⁠/ Photo: Spain

Jama’a a birnin Madrid na kasar Sifaniya ne sun taru a gaban ginin ma’aikatar harkokin wajen kasar domin nuna adawa da harin jiragen yakin Isra’ila suka kai a asibitin Al-Ahli Baptist da ke Gaza.

Jama'a sun taru a dandalin Bascarsija domin nuna adawa da harin da Isra'ila ta kai asibitin Baptist na Al-Ahli da ke Gaza/ Hoto: AA

Jama'a sun taru a dandalin Bascarsija domin nuna adawa da harin da Isra'ila ta kai asibitin Baptist na Al-Ahli da ke Gaza.

Jama'a a birnin New York suka hallara domin nuna adawa da harin jiragen Isra'ila kan asibitin Al-Ahli Baptist da ke Gaza. Photo: AA

Jama'a a birnin New York suka hallara domin nuna adawa da harin jiragen Isra'ila kan asibitin Al-Ahli Baptist da ke Gaza.

Daga cikin mutanen har da Mambobin Yahudawa mabiya darikar gargajiya ta Orthodox masu adawa da kungiyar yada akidar Yaduwa ta Zionism su ma sun halarci zanga-zangar.

TRT World