Ga mutanen Gaza da suka tsira da ransu a yakin Gaza, dole ne rayuwa ta ci gaba.
Gari na wayewa ake layin sayen biredi da sauran kayan masarufi duk da harin bama-bamai da Isra'ila ke ci gaba da kai wa yankin.
Hukumomin Isra'ila sun katse wutar lantarki da ruwa da kuma hanyoyin samar da abinci a wani bangare na "mamaye yankin baki daya" yayin da rikicin yankin ke dada kamari.
Jami'an tsaron Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza inda suka kashe Falasdinawa sama da 5000 tare da jikkata kimanin mutum13,000 a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu.
Falasdinawa suna halin tsaka-mai-wuya, ba wai ta neman hanyar tsira daga bama-bamai da ake harba musu kadai ba har ma da rashin kayan masarufi da za su a bakin salati.
An yi ta kira kan a tsagaita wuta domin ba da damar kai kayan agaji ga al'ummar Gaza.