1616 GMT — Mutum 50 ne suka mutu sakamakon harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a wasu makarantu biyu a Gaza
Akalla mutum 50 ne suka mutu sannan wasu ɗaruruwa suka jikkata sakamakon harin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai kan wasu makarantu biyu da Falasdinawa ke samun mafaka a Zirin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Wafa.
Wafa ya rawaito cewa jiragen yakin Isra'ila da manyan bindigogi sun yi luguden wuta kan makarantar Salah Ad-Din da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya da kuma makarantar Shahidi Assad Safwati da ke unguwar Al Darraj.
1451 GMT — Kusan Falasdinawa miliyan 1.9 sun rasa matsugunansu a fadin Gaza - MDD
Kusan mutane miliyan 1.9, ko sama da kashi 80 na al'ummar kasar, sun rasa matsugunansu a fadin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, in ji hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu, UNRWA.
Ya kara da cewa, ya zuwa ranar 2 ga watan Disamba, ma'aikatan UNRWA 111 ne aka kashe tun farkon yakin Isra'ila a kan yankin Falasdinu.
Da sanyin safiyar Juma'a ne sojojin Isra'ila suka sake kai hare-hare a Zirin Gaza bayan ayyana kawo karshen dakatar da ayyukan jinƙai na tsawon mako guda.
1340 GMT — Hare-haren Isra'ila a Gaza 'na ƙara tsananta ga yara da iyaye mata': UNICEF
Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda tashe-tashen hankula ke ƙara ƙamari a yankin kudancin Gaza, inda mai magana da yawunsa ya ce hare-haren suna da muni kamar yadda aka sha fama da su a arewacin kasar.
"Duk da abin da aka tabbatar, hare-haren da aka kai a kudancin Gaza suna da muni kamar yadda ya faru a arewa. Ko ta yaya, abin yana kara ta'azzara ga yara da iyaye mata," in ji mai magana da yawun UNICEF James Elder a ranar Litinin a X.
"Muryarku tana da mahimmanci. Dole ne mu yi imani cewa za mu iya zama wani bangare na dakatar da yakin da ake yi a kan yara... Yin shiru ba zai yi mana komai ba," in ji shi.
Da sanyin safiyar Juma'a ne sojojin Isra'ila suka sake kai hare-hare a Zirin Gaza bayan ayyana kawo karshen tsagaita wuta da aka yi na tsawon mako guda.
1304 GMT — Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasdinawa 30 a arewacin Gaza
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu ya rawaito cewa aƙalla mutum 30 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a arewacin Gaza.
Gaba daya Falasdinawa 15,899 ne aka kashe a hare-haren Isra'ila a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, kashi 70 cikin 100 cikinsu mata ne da ƙananan yara, in ji kakakin ma'aikatar lafiya ta Falasdinu da ke Gaza.
Sojojin Isra'ila za su yi 'yaki sosai' a kudancin Gaza
Rundunar sojin Isra’ila ta ce an an raunata sojojinta uku a wani hari da aka kai musu daga kasar Lebanon a wani sansaninsu da ke arewacin Isra’ila.
Isra’ila ta ce an harba musu rokokin ne a a yayin da sojojinta ke a sansaninsu da ke birnin Yiftah, inda ta ce sojojin nata sun mayar da martani ta hanyar harba makamai daga gefen da harin ya fito.
Ana samun rikici tsakanin sojojin Isra’ila da kuma mayakan Hezbollah na Lebanon inda suke ci gaba da kai wa juna hari tun bayan da aka soma rikici tsakanin Gaza da Isra’ila.
1345 GMT — Qatar za ta ci gaba da kokarin dawo da tattaunawar sulhu don tsagaita wuta a Gaza: Firaiminista
Qatar za ta ci gaba da kokarinta da sauran kasashen duniya na dawo da tattaunawar sulhu don tsagaita wuta a Gaza da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta
Firaiminista kuma Ministan Harkokin Waje Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani ya bayyana a cikin jawabinsa yayin taron Majalisar Ministoci karo na 158 na zaman taro na 44 na kasar Qatar ya ce: "Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta sanar da cewa, an gudanar da taron koli na kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf (GCC) a birnin Doha."
Al Thani ya sake nanata cewa "Qatar ta yi Allah wadai da laifuffukan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta aikata tare da yin kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa cikin gaggawa ba tare da nuna son kai ba kan wadannan laifuka, musamman hare-haren da aka kai kan fararen hula, da agaji da wuraren jinkai."
0130 GMT — Matasa da mata a Amurka suna adawa da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza
Galibin mata da matasa na Amurka ba su amince da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza ba, kamar yadda wani bincike da wata kungiya mai ra'ayin mazan jiya mai cibiya a Amurka, Gallup ta yi a kan mutum 1,013 ya nuna.
Sakamakon binciken da aka gudanar a watan jiya kuma aka fitar a wannan makon ya nuna cewa kashi 52 cikin 100 na mata da kashi 67 cikin 100 na matasa masu shekaru 18 zuwa 34 ba sa goyon bayan hare-haren Isra'ila.
Yayin da kashi 44 cikin 100 na mata ke goyon bayan hare-haren Isra'ila, wannan adadi ya karu zuwa kashi 59 na maza, yayin da kashi 37 cikin 1000 na matasa maza ke adawa da hare-haren.
Bakaken fata da Hispayawa da mutanen Asiya da na Tsibirin Pacific da ’Yan asalin ƙasar Amurka ba sa goyon bayan hare-haren da kashi 64 cikin ɗari, yayin da kashi 61 cikin 100 na fararen fata ke goyon bayan hakan.
A bangaren jam'iyyu kuwa, kashi 63 cikin 100 na 'yan Democrat ba su amince da harin da Isra'ila ke kai wa ba, inda kashi 36 cikin 100 ke goyon bayanta, yayin da kashi 71 cikin 100 na 'yan jam'iyyar Republican suka nuna amincewarsu, yayin da kashi 23 ne kawai suka ki amincewa.
0100 GMT — Sojojin Isra'ila za su yi 'yaki sosai' a kudancin Gaza
Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta za su yi yaki da mayakan Hamas a kudancin Gaza “kamar yadda suka yi a arewaci.”
"Mun yi yaki sosai kuma cikakke a arewacin Gaza kuma za mu yi hakan a kudanci,” in ji Shugaban Rundunar Sojin Isra'ila Herzi Halevi.
Halevi ya kai “ziyara ga Rundunar da ke Gaza inda ya tattauna da sojojin da ke can,” a cewar wata sanara da sojojin suka fitar.
A gefe guda, Gidan Rediyon Sojin Isra'ila ya bayar da rahoton cewa sojojin sun soma kai hari ta kasa a kudancin Gaza.
Ya ce sun soma kai hare-haren da daga arewacin Khan Yunis.
0030 GMT — Kungiyar Houthi a Yemen ta ce ta kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila 2 a Bahar Maliya
Kungiyar Houthi ta kasar Yemen ta ce ta kai hari da rokokin ruwa da jirgi mara matuki kan jiragen ruwan Isra'ila biyu a Zirin Bab al Mandab da ke Bahar Maliya.
“Dakarun Rundunar Sojojin Ruwa na Yemen sun kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila biyu a Zirin Bab Al Mandab, masu suna Unity Explorer da jirgi Number Nine, inda aka kai hari da rokokin ruwa kan jirgin ruwan farko sannan aka kai hari da jirgi mara matuki a kan jirgin ruwa na biyu,” a cewar kakakin rundunar Yahya Saree.
Saree ya ce “an kai harin ne bayan jiragen ruwan biyu sun ki sauraren gargadin da Rundunar Sojin Ruwan Yemen ta yi musu.”
“Rundunar Sojojin Yemen tana ci gaba da hana jiragen ruwan Isra'ila daga yin kara-kaina a Bahar Maliya da Kogunan Yankin Larabawa har sai Isra'ila ta daina kai hare-hare kan 'yan uwanmu da ke Gaza,” in ji shi.