Harin bama-bamai da Isra’ila take kai wa makarantu na nuna shirinta na korar Falasɗinawa: Hamas

Harin bama-bamai da Isra’ila take kai wa makarantu na nuna shirinta na korar Falasɗinawa: Hamas

Ƙungiyar ta gwagwarmaya ta ce "an shafe fiye da mako biyu babu wani agaji da ya shiga Gaza."
Tawagar Kare Al’umma ta Falasɗinu tana bincike tare da ceto a Makarantar Asmaa bayan harin Isra’ila a sansanin ‘yan gudun hijira na Shati a Birnin Gaza, Gaza, ranar 19 ga Oktoba. / Hoto: AA

Ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinu Hamas ta ce harin da sojojin Isra’ila suka kai makarantu biyu a arewacin Gaza da Birnin Gaza sun tabbatar da shirin Tel Aviv na korar Falasɗinawa.

"Sababbin hare-haren da ‘yan mamaya suka kai Makarantar Abu Hussein, wacce ta zama matsugunni ga mutanen da suka yaƙi ya raba da gidajensu a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia a arewacin, da harba bindigogin atilare irin na kan mai uwa-da-wabi kwanaki biyu kawai bayan kisan ƙare-dangi a can, tare da jefa bama-bamai a wata makarantar a yammacin Birnin Gaza, sun tabbatar da shirin masu mamaya na korar mutanenmu ta hanyar kashe-kashe da aiwatar da kisan ƙare-dangi,” a cewar ƙungiyar ta Falasɗinawa a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.

Hamas ta yi kira ga ƙasashen Larabawa da na Musulmai su “ɗauki haƙƙin da ke kansu a tarihi na goyon bayan jajircewar mutanenmu da tsayar da kisan ƙare-dangi da Isra’ila ke yi, wanda yake da mummunan tasiri da barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.

Ta kuma jaddada cewa, an shafe fiye da mako biyu babu wani agaji da ya shiga Gaza, musamman ma sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia, tare da sauran unguwannin da ke kusa da shi, a lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare yankin.

“A zahiri ɗan abin da bai kai ya kawo ba ne kawai ya shiga Birnin Gaza kaɗai, wanda shi ma wani yanki ne da ke fama da bala’i ya ke kuma buƙatar agaji,” a cewarta.

Hamas ta kuma buƙaci Larabawa da kafofin watsa labarai na duniya su ringa “fallasa labaran ƙarya da kafofin watsa labaran Isra’ila ke bayarwa da farfagandarsu ta ƙarya dangane da shigar da agaji Gaza.”

Aƙalla Falasɗinawa bakwai ciki har mata da yara aka kashe ranar Asabar a wani hari ta sama da Isra’ila ta kai makarantar Asmaa wacce Hukumar Agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya ke gudanarwa a yammacin Gaza, wacce ta zama matsugunni ga iyalan da yaƙi ya raba da gidajensu.

Isra’ila ta kashe fiye da mutane 42,500 a Gaza tun bayan harin kan iyaka da Hamas ta kai zuwa Isra’ila. Ta kashe shugaban ƙungiyar Yahya Sinwar a cikin wannan makon. Sinwar ya zama shugaba bayan kashe Ismai’ila Haniyeh ranar 31 ga watan Yuli a Tehran.

TRT World