Binciken ya ce kimanin mutum 450,000 ke mutuwa a duk shekara daga cutar da ke da alaƙa da gurɓatacciyar iska daga tsakanin shekarar 2000 da 2019. / Hoto: AP Archive

Wani sabon rahoto sa aka fitar a ranar Alhamis ya alaƙanta gurɓacewar iska sakamakon gobara da mutuwar fiye da mutum 1.5 a shekara a faɗin duniya, inda hakan ya fi faruwa a ƙasashen da ke tasowa.

Ana sa ran adadin mutanen da ke mutuwa zai karu nan da shekaru masu zuwa yayin da sauyin yanayi ke sa gobarar daji ta yawaita kuma ta yi tsanani, a cewar binciken wanda aka wallafa a Mujallar Lancet.

Tawagar masu bincike ta kasa da kasa sun duba bayanan da ake da su a kan "gobarar da ake samu", wadanda suka hada da gobarar daji da sauyin yanayin ke ci gaba da jawo ta da kuma shirya gobarar da an’adam ke ta da ita kamar ta kokarin kona ciyayi a gona.

Binciken ya ce kimanin mutum 450,000 ke mutuwa a duk shekara daga cutar da ke da alaƙa da gurɓatacciyar iska daga tsakanin shekarar 2000 da 2019.

An kuma danganta wasu mace-macen mutane 220,000 daga cututtukan numfashi da hayaƙi da kuma ɓurɓushin da gobara take yaɗawa a cikin iska.

Ƙasashen da suka fi fama da matsalar

Daga dukkan abubuwan da ke faruwa a duniya, adadin mutuwar mutum miliyan 1.53 a kowace shekara yana da alaƙa da gurɓatacciyar iska daga gobarar yanayi, a cewar binciken.

Fiye da kashi 90 cikin 100 na wadannan mace-mace sun kasance a kasashe masu ƙaramin ƙarfi da matsakaicin kudin shiga, in ji shi, kusan kashi 40 cikin 100 a yankin kudu da hamadar Sahara kadai.

Kasashen da aka fi samun adadin wadanda suka mutu sun hada da China da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Indiya da Indonesia da Nijeriya.

An zargi wani adadi na ƙone-ƙone da aka yi ba bisa ƙa'ida ba a gonaki a arewacin Indiya da mummunan hayaki da ake shake babban birnin New Delhi kwanan nan da jawo matsalar.

Marubutan binciken na Lancet sun yi kira da a dauki matakin gaggawa don magance yawan mace-mace sakamakon gobarar da ke tashi a fadin duniya.

Bambancin da ke tsakanin kasashe masu arziki da matalauta na ƙara nuna rashin adalci a sauyin yanayi, inda wadanda ba su faye jawo ɗumamar yanayi ba suka fi fama da illarsa.

Wasu daga cikin hanyoyin da mutane za su iya guje wa hayaki daga gobara - kamar ƙaura daga yankin da yin amfani da na'urorin tsabtace iska da abin rufe fuska, ko zama a gida - ba sa samuwa ga mutane a cikin ƙasashe masu fama da talauci, in ji masu binciken.

Don haka sun yi kira da a kara tallafin kudi da fasaha ga mutanen da ke cikin kasashen da matsalar ta fi shafa.

An fitar da binciken ne mako guda bayan tattaunawar sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya inda wakilai suka amince da kara samar da kudaden tallafin da kasashe masu tasowa suka yi zargin cewa bai wadatar ba.

Hakan na zuwa ne bayan da Ecuador ta ayyana dokar ta baci kan gobarar dazuzzukan da ta yi barna a sama da hekta 10,000 a kudancin kasar.

Haka kuma duniya ta fuskanci mahaukaciyar guguwa da fari da ambaliya da sauran munanan yanayi a lokacin da ake sa ran za ta kasance shekara mafi zafi a tarihi.

AFP