Gomman mutane ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani ginin bene mai hawa biyar a tsakiyar birnin Johannesburg ranar Laraba da daddare, a cewar sanarwar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta babban birnin na Afirka ta Kudu.
Kazalika mutane da dama sun jikkata yayin da wasu ke cikin mawuyanci yanayi sakamokon shakar hayakin gobarar.
Tuni dai aka garzaya da su asibiti domin ba su kulawa, in ji kakakin hukumar ta bayar da agajin gaggawa Robert Mulaudzi.
"Mun kirga gawarwakin mutane 60, wadanda muka samu ya zuwa yanzu sai kuma karin wasu mutane 43 da suka samu kananan raunuka," a cewar Mulaudzi yayin da yake zanta wa da kafar yada labaran kasar ta ENCA.
Jami’an kwana-kwana sun kashe gobarar yayin da suke ci gaba da neman mutanen da gobarar ta rutsa da su.
"Muna duba kowane hawa a cikin ginin benen don gano gawarwakin," a cewar Mulaudzi, inda ya kara da cewa ana sa ran adadin wadanda suka mutu ya iya karuwa.
Kawo yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar cikin dare ba.
Ginin da ya zuwa yanzu ake kan kwashe mutanen ciki yana yankin da ya taba kasancewa wurin kasuwanci ne a babban birnin na kasar Afirka ta Kudu, kuma ana amfani da wajen a matsayin wani matsuguni na yau da kullun, in ji Mulaudzi.
Hotunan da aka yada ta talabijin sun nuna yadda motocin kashe gobara da motocin daukar marasa lafiya ke wajen ginin mai launin ja da fari da kuma yadda tagogin ginin suka kone kurmus.