Makokin mutanen da suka mutu sakamakon gobara da tashi a wajen wani biki a Hamdaniya da ke Iraƙi. / Hoto: Reuters

Mutanen da suka tsira daga gobarar da ta tashi a wurin wani bikin a kasar Iraƙi da masu makokin akalla mutane 100 da suka mutu a sanadiyar iftila'in sun cika makil domin binne mamatan a ranar Alhamis, kwana biyu bayan aukuwar lamarin.

Masu makokin sun shiga ɗimuwa tare da rungume junansu a jikin ginin cocin Katolika na Al-Tarera inda aka jera hotunan mamatan, maza da mata har da ƙananan yara masu mabambantan shekaru.

"Ban san abin da zan ce ba; muna jin zafi sosai a cikin zuƙatanmu, ba za mu taba mantawa da wannan iftila'i ba," in ji Najiba Yuhana, mai shekara 55, wacce ta rasa 'yan uwanta da dama.

"Akwai tashin hankali da baƙin ciki mara misaltuwa," in ji ta.

Hukumomi a kasar sun ɗora laifin wasan wutar da ya sanadiyar kama kwalliyar rufin ɗakin bikin da aka ƙayatar da kayayyaki masu saurin ci da wuta.

Baƙin da suka firgita

Akalla mutum 150 ne suka samu rauni na ƙuna da shaƙar hayaƙin gobarar da kuma turmutsitsin ginin da ya firgita kusan baƙi 900 da suka yi kokarin tserewa daga kofofin da aka ware don tsira a wurin.

Iftila'in ya afku ne a garin Qaraqosh, da ke zama cibiyar al'umma mabiya addinin Kirista marasa rinjaye da yake yankin Nineveh kusa da birnin Mosul, wanda har yanzu yake farfadowa daga ayyukan ta'addacin ƴan ƙungiyar Daesh da ISIS a shekarar 2014 zuwa 2017.

Cibiyar kananan mabiya addinin Kirista ta kasar Iraƙi na yankin Nineveh da ke kusa da birnin Mosul, wanda har yanzu ke farfadowa daga ta'addancin mulkin kungiyar Daesh/IS daga shekara ta 2014 zuwa 2017.

Garin, wanda kuma ake kiransa da Hamdaniyah, a yanzu haka ya zama gida ga al'ummar Kiristoci 26,000 - kusan rabin yawan mutanensa na asali.

Ana ta koke-koke a cikin cocin, wanda Fafaroma Francis ya taba ziyarta a watan Maris na shekarar 2021, inda ya cika da ƴan uwan wadanda suka mutu tare da wadanda suka tsira kuma suka ji rauni daga lamarin.

Makoki na ƙasa

Firaiminista Mohamed Iraki Shia al-Sudani, ya ayyana kwana uku na zaman makoki a kasar, ya kuma yi tattaki zuwa lardin a ranar Alhamis don ziyartar "wadanda suka jikkata da kuma iyalan wadanda abin ya shafa", a cewar sanarwar ofishinsa.

An dai shiga rudani da tashin hankali sakamakon yawan adadin mace-macen da aka samu a iftila'in, wanda hukumomi suka ɗora alhakinsa a kan rashin kiyaye ƙa'idojin tsaro da rashin isassun hanyoyin fita don tsira a wajen da kuma amfani da kayan gini masu saurin ci da wuta.

Hukumomin kasar sun kama mutum 14 - mamallakin wurin da ma'aikata 10 da kuma wasu mutum uku da ake zargi da tayar da wutar, a cewar Ministan Cikin Gida na Kasar.

Sau da dama ana ƙin kiyaye ƙa'idojin tsaro a Iraƙi, kasar da har yanzu ke ƙoƙarin farfaɗowa daga mulkin kama-karya da yaƙi da tashe-tashen hankula da ake ci gaba da fama da kuma rashin shugabanci, ga cin hanci da rashawa da kuma lalacewar ababen more rayuwa.

TRT World