Kotun hukunta manyan laifuka za ta yanke hukuncin farko kan shari’ar da Afirka Kudu da wasu kasashe suka shigar kan Isra’ila game da kisan kare-dangin da take yi a Gaza da aka yi wa kawanya, wani muhimmin hukunci da dauki hankalin yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICJ) za ta iya ba da umarni ga Isra'ila ta dakatar da yakin da take yi a Gaza ko kuma ta bayar da damar da za ta saukaka ayyukan jinkai.
Ko da yake kotun ba za ta yanke hukunci kan ko da gaske Isra'ila na aikata kisan kare-dangi a Gaza ko akasin hakan ba a hukuncin da za ta yanke a ranar Juma'a.
A wannan matakin, Kotun ICJ za ta ba da umarnin gaggawa kafin yin la'akari da manyan zarge-zarge da ke kan Isra'ila na aikata kisan kare-dangi a Gaza - tsarin da aka iya daukar tsawon shekaru.
"Afirka ta Kudu ba ta bukatar ta tabbatar da cewa Isra'ila na aikata laifukan kisan kiyashi," a cewar Juliette McIntyre wata kwararriya a fannin shari'ar kasa da kasa daga jami'ar South Australia.
Afirka ta Kudu ta kawo wannan batu ne kan cewa Isra'ila ta karya doka ta hana kisan kare-dangi ta Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 1948, wadda aka kafa bayan Yakin Duniya na Biyu da na kisan kare-dangi a Turai.
"Suna bukatar kawai su tabbatar da cewa akwai yiwuwar fadawa hatsarin kisan kare-dangi," kamar yadda ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Bayan zaman sauraron kararrakin na kwanaki biyu a farkon wannan watan a fadar zaman lafiya MDD da ke birnin Hague, wurin da ke nesa da zaluncin isra'ila a Gaza, ya hada lauyoyi gardama tare da muhawara kan yarjejeniyar dokar kisan kare-dangi.
"Ba a taba tabbatar da batun kisan kiyashi da wuri ba," kamar yadda Adila Hassim wata babbar Lauyar Afirka ta Kudu ta shaida.
"Amma wannan Kotun tana da wasu manyan shaidu da aka tattaro na makonni 13 da suka wuce, wandanda karara suka nuna abubuwan da suka faru tare da wasu manufofi da suka tabbatar da ikirarin aikata kisan kare dangi," in ji ta.
'Duniya ta kife kasa'
Wannan lamari dai ya futasa Isra'ila, inda firaiministan kasar Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa "Duniya ta kife kasa".
Lauyan Isra'ila, Tal Becker, ya yi watsi da shari'ar Pretoria a matsayin wani "babban rashin gaskiya da take shari'a" da kuma "shafe ainihin abubuwan da suka faru "a kasa.
Hukunce-hukuncen da kotun ta ICJ ya shafi dukkan bangarorin, sai dai ba da da nauyin aiwatar da su.
A wasu lokutan, akan yi watsi da su gaba daya - alal misali, kamar yadda kotun ta umarci Rasha ta dakatar da hare-haren da take kaiwa Ukraine.
Tuni dai Netanyahu ya shaida cewa ba ya tsoron kamun kotu, yana mai cewa, ''babu wanda zai hana mu - ba Hague ba, ba kuma barazanar wasu kasashe ''Axis of Evil'' ba ko kuma wani ba''.
'Babban tasiri'
"An yi hasashe kan cewa umurnin kotun ba zai yi wani tasiri sosai kan ayyukan sojin Isra'ila ba," a cewar Cecily Rose, mataimakiyar farfesa a fannin dokokin kasa da kasa a jami'ar Leiden.
Sai dai idan har kotun ta yanke hukunci kan cewa akwai yuwuwar barazanar kisan kare-dangi a Gaza, to hakan na iya yin tasiri sosai, musamman ga sauran kasashen da ke goyon bayan Isra'ila a siyasance ko ta soji.
"Zai yi matukar wuya sauran kasashe su ci gaba da goyon bayan Isra'ila idan har aka samu wasu bayanai daga bangare na uku kan akwai yiwuwar hadarin kisan kare dangi," in ji McIntyre.
Kwararriya ta yi kari da cewa "akwai yiwuwar kasashe su janye tallafinsu na soji ko kuma duk wasu taimako da suke baiwa Isra'ila domin kaucewa hakan."
Kazalika, ta bayyana cewa tasiri "babban" kan duk hukunci da za a dauka kan Isra'ila karkashin yarjejeniyar kisan kare dangi, idan aka yi la'akari da mummunan tarihin da ta kunsa.
A bayanan da ta gabata wa kotun, Afirka ta Kudu ta dauki ''nauyin alhakin'' zargin Isra'ila da kisan kare dangin, amma ta ce za ta tsaya ta bi ka'idojin da ke karkashin yarjejeniyar doka.
Kawo yanzu dai Isra'ila ta kashe Falasdinawa 25,900 tare da jikkata mutum 64,110 a mummunan hare-haren da take kaiwa yankin Gaza da ta yi wa kawanya.
Kazalika yakin na Isra'ila ya raba kusan kashi 90 cikin 100 na Falasdinawa da ke zaune a yankunan da aka killace daga matsugunansu, kuma mafi yawansu na fama da karancin abinci, a cewar MDD.
Kalaman da ministocin Isra'ila masu tsatsauran ra'ayi suka yi na yin kira kan a shafe Falasdinawa da ke Gaza da matsugunan Yahudawa da ke zama ba bisa ka'ida ba a can ko kuma a jefa bam din nukiliya a zirin Gaza, su ma sun jawo kakkausar suka daga duniya, hakan na daya daga cikin hujjojin da Afirka ta Kudu ta gabatar a Hague.