Erdogan ya jaddada matsayin Turkiyya na haɗa kawunan ƙasashen Musulmai tare da ƙara adadin ƙasashen da za su amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta./Hoto:AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga ƙasashen duniya su ɗauki matakin bai-ɗaya wajen kawo ƙarshen hare-haren Isra'ila na "shan jinin" Falasɗinawa da gallaza musu.

Da yake gabatar da jawabi ga mambobin jam'iyyar Justice and Development (AK) ranar Litinin ta manhajar bidiyo domin bikin Babbar Sallah, Erdogan ya ce Falasɗinawa, waɗanda suka kwashe fiye da shekara 76 suna fuskantar bala'i da mamaya daga Isra'ila, sun yi Babbar Sallah cikin baƙin-ciki kuma suna buƙatar zaman lafiya.

“A matsayinmu na al'ummar Musulmai, muna jin raɗaɗin kisan kiyashin da Isra'ila ta yi wa 'yan'uwanmu 38,000. Muna fuskantar jarrabawa a matsayinmu na Musulmai kuma 'yan'adam. Ya zama wajibi mu ɗauki mataki kan kisan da ake yi wa 'yan'uwanmu a Gaza.

"Dole ƙasashen duniya su ɗauki matakin dakatar da Isra'ila daga shan jini da kuma hana ta ci gaba da kisan ƙare-dangi da take yi kullum nan-take," in ji shi.

Kazalika shugaban Turkiyya ya soki gwamnatin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu game da jefa ɗaukacin yankin cikin bala'i, ciki har da 'yan ƙasarsu, domin cim ma muradunsu na siyasa. “Mun bayyana matsayarmu ƙarara a makon jiya lokacin da muka ziyarci Sifaniya da kuma a wurin taron shugabannin ƙungiyar ƙasashen G7 da aka yi a Italiya.”

“Ba za mu yi gum da bakinmu ba"

Ya ƙara da cewa, "A matsayinmu na ƙasar Turkiyya, mun fito da dukkan ƙarfinmu domin wanzar da zaman lafiya a yankin sannan mu tabbatar an hukunta masu hannu a kisan kiyashi."

Shugaba Erdogan ya ce mahukunta a Ankara sun bi sahun sauran ƙasashen duniya wajen shigar da Isra'ila ƙara a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya game da kisan kiyashi, tare da dakatar da kasuwanci da Isra'ila, domin matsa lamba kanta har sai ta daina kashe-kashen da take yi a Gaza.

Erdogan ya jaddada matsayin Turkiyya na haɗa kawunan ƙasashen Musulmai tare da ƙara adadin ƙasashen da za su amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

“Ba za mu yi gum da bakinmu game da bala'in da ke aukuwa a sauran ƙasashen Musulmai da kuma Gaza ba.Muna ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a Sudan wanda aka kwashe fiye da shekara guda ana yi. Muna yin gaggawar kai agaji a duk inda ake fuskantar rikici daga Libya zuwa Somalia, daga Afghanistan zuwa Yemen.”

TRT World