Duniyarmu ta Earth na dab da fadawa hatsari tana kaucewa daga muhallinta mai aminci

Duniyarmu ta Earth na dab da fadawa hatsari tana kaucewa daga muhallinta mai aminci

"Hakan na nufin doron duniyarmu na rasa karfinsa, kuma muna jefa amincinta a cikin hadari."
"Har yanzu muna tafiya ne a kan kuskure," a cewar Johan Rockstrom da shi ma aka wallafa binciken da shi. Hoto: AFP

Ayyukan da 'yan'adam suke yi a doron kasa suna sa karfin duniyarmu ta Earth yana raguwa, lamarin da ke matsar da ita can nesa da "inda take zaune cikin aminci a sararin samaniya" yankin da a nan ne kawai halittu ciki har da 'yan'adam za su iya rayuwa, a cewar wani gagarumin bincike.

Shida daga cikin ayyuka tara da suka sanya duniya shiga wancan bigire mai hatsari su ne -- sauyin yanayi da sare dazuzzuka da karewar wasu nau'in halittu da sinadarai masu karfi da kafewar tekuna da kuma amfani da sinadarin nitirojin, kamar yadda wata tawagar masana kimiyya 29 ta fada a ranar Laraba.

Biyu daga cikin sauran ukun -- gurbacewar teku da kurar da ke baibaye sararin samaniya -- su ma suna dab da kara munana lamarin, inda shigifar sararin duniya ce kawai a yanzu ba ta fuskantar wata matsala sosai.

Wajen da duniyar take cikin aminci ya nuna "matakai masu muhimmanci da ke tabbatar da duniyar Earth a yanayin da take zaune lafiya fiye da shekara 10,000, daidai lokacin da dan'adam da wayewar zamani suka bunkasa," a cewar jagorar binciken Katherine Richardson, wata farfesa a Jami'ar Copenhagen.

Binciken shi ne bayani na biyu mafi girma a kan lamarin, inda aka fara kaddamar da shi a shekarar 2009 a lokacin da aka samu tsananin dumamar yanayi a duniya da yawan karewar wasu halittu da har lamarin ya wuce kima.

"Har yanzu muna tafiya ne a kan kuskure," a cewar Johan Rockstrom da shi ma aka wallafa binciken da shi, kuma darakta a Cibiyar Binciken Tasirin Sauyin Yanayi ta (PIK).

"Kuma babu wata alama da ke nuna cewa iyakokin duniyar babu wanda yake zaune lafiya, in ban da shigifar sararin duniya, wacce ita ma ta samu lafiya ne tun bayan haramta amfani da sinadaran da ke lalata ta, har ta fara komawa daidai," ya shaida wa 'yan jarida a wani taron manema labarai.

"Hakan na nufin doron duniyarmu na rasa karfinta, kuma muna saka amincinta a cikin hadari."

Binciken ya auna tasirin ayyukan tara da suke yi wa tsarin duniyar barazana.

Muna dab da shiga hatsari

Kan batun karewar wasu nau'in halittu, idan har aka ci gaba da tafiya a kan turbar raguwar bacewar halittu sau 10 fiye da shekara miliyan 10 baya, to lallai hakan abin so ne.

Sai dai a zahiri, yawan halittun da ke bacewa na karuwa da sauri akalla sau 100 fiye da yadda ya kamata.

"Kan batun sauyin yanayi kuwa, muna kan turbar da baro-baro tana kai mu ga halaka ne, wani yanki da dunya ba ta taba gani ba a shekara miyan hudu da suka gabata" in ji Rockstrom.

"Babu wata hujja da ke nuna cewa 'yan'adam za su iya rayuwa a muhallin ba," ya kara da cewa.

A sabon binciken a karon farko an auna tare da gano yadda dubban sinadarai da dan'adam ke samar da su daga robobi da maganin kwari zuwa dattin makamahin nukiliya da magunguna da suke barnata muhalli - sun wuce iyaka inda suke zama hatsari.

Kazalika an gano yadda ruwan teku da na koguna da wanda ake samu daga yashi da tsirrai duka ke janyewa.

Wani muhimmin abu da aka gani shi ne na yadda ayyuka masu hatsarin suke bunkasa ta wajen haduwa da juna.

AFP