1540 GMT — Birtaniya da Faransa sun jaddada aniyarsu kan samar da kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya
Birtaniya da Faransa a ranar Lahadi sun sake jaddada aniyarsu ta ganin an samar da kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya – daya ta Isra’ila daya ta Falasdinu. Sun bayyana haka ne a wata sanarwa da fadar Firaiministan Birtaniya ta fitar a ranar Lahadi.
Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak da Emmanuel Macron na Faransa sun kuma jaddada bukatar kai kayan agaji cikin Gaza.
Haka kuma sun bayyana cewa za su yi aiki tare domin kai kayayyakin da ake bukata cikin gaggawa kamar abinci da man fetur da magunguna a cikin Gaza.
1450 GMT — Isra'ila ta kashe 'yan jarida 34 a Gaza zuwa yanzu
‘Yan jarida 34 ne Isra’ila ta kashe zuwa yanzu a hare-haren da take kaiwa a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba.
A wata sanarwa, ma’aikatar lafiya da ke Gaza ta saki adadin ‘yan jarida da aka kashe a Gaza a hare-haren da Isra’ilar ke kaiwa tsawon kwanaki 23.
‘Yan jaridar Falasdinu 34, daga ciki har da mata uku suka rasa ransu a hare-haren, haka kuma ‘yan jarida da dama sun rasa iyalansu sakamakon hare-haren Isra’ila.
1300 GMT — MDD ta rasa ma'aikatanta 59 a Gaza
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya reshen Falasdinu ta ce ma’aikatanta 59 aka kashe zuwa yanzu a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba.
Hukumar ta gudanar da taron adduo’i a Gaza kan ma’aikatan nata da aka kashe.
Hukumar ta koka kan yadda ake samun karuwar wahala da kuma yadda take ci gaba da rasa ma’aikatanta.
1030 GMT — Dubban mutane sun fasa dakunan ajiyar kayayyaki na MDD a Gaza
Dubban mutane sun fasa dakunan ajiyar kayayyakin agaji na Majalisar Dinkin Duniya da ke Gaza, kamar yadda majalisar ta bayyana a ranar Lahadi.
Majalisar ta ce mutanen sun kwashi fulawa da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.
Thomas White wanda darakta ne a hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce fasa dakunan ajiyar wata alama ce da ke nuna doka da oda ta soma yankewa sakamakon matsi da jama’a ke ciki.
0950 GMT — Isra'ila ta na yi wa asibitin Al Quds na Gaza barazana
Kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta bayyana hukumomin Isra’ila sun mata babbar barazana kan cewa su tattara su bar asibitin Al Quds da ke Gaza sakamakon suna da niyyar kai masa hari.
“Tun da safe, an ta kai hare-hare mita 50 daga asibitin,” a wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafin X.
0925 GMT — Isra'ila ta kai hari ta sama kusa da asibiti mafi girma a Gaza
Isra’ila ta kai hari kusa da asibiti mafi girma da ke Gaza, kamar yadda mazauna suka tabbatar.
Mazaunan sun ce harin da Isra’ila ta kai ya lalata hanyoyin da za su kai ga asibitin, wanda asibitin ya kasance wata mafaka ga dumbin Falasdinawa da ke guje wa hare-haren Isra’ila.
Wannan na zuwa ne yayin da Isra’ilar ke ci gaba da zafafa hare-hare a Gaza.