Kasashen Turai sun mayar da saka hijabi ko gyale wani batu na nuna wariya a nahiyar a tsawon shakaru. / Hoto: Taskar AA  

Babbar Kotun Tarayyar Turai ta yanke hukunci cewa hukumomin gwamnati a kasashe mambobin kungiyar za su iya haramta wa ma'aikata sanya alamomin addini, kamar hijabi ko gyale da mata Musulmai suke sanyawa.

A ranar Talata ne, Kotun Shari'a ta Tarayyar Turai (CJEU) ta bayyana cewa manufar da ke nuna rashin sanya addini wajen gudanar da mulki tana da amfani.

Kotun ta kuma ƙara da cewa wata gwamnatin za ta iya kafa hujja kan wannan mataki idan ta zabi yin hakan kan dukkan al'umarta ba tare da nuna bambanci a sanya alamun da suka shafi addini ko wani abu da aka yi imani a kai ba.

Kotun ta jaddada cewa hukumomin kasashe mambobin kungiyar suna da ikon tsara duk wani mataki da ya dace a ayyukan da suke son tabbarta kan al'ummarsu.

Duk da haka, dole ne a ci gaba da bin wannan manufa bisa tsari sannan dole a takaita matakai kan abubuwan da suka dace a yi su, in ji kotun.

Tabbatar da yin hakan yana karkashin ikon babbar kotun kasa, wajen tabbatar da ganin an bi ƙa'idojin da ake bukata.

Matakin nuna wariyar ya shafi tufafin mata Musulmai

Lamarin ya zo gaban babban kotun CJEU ne bayan hana wata ma’aikaciyar karamar hukumar Ans da ke yankin gabashin kasar Belgium shiga wurin aikin sanye da lullubi.

Daga baya karamar hukumar ta sauya sharudda da tsarin aikin ma'aikatanta inda ta bukace su da su bi tsattsauran ra'ayi nan ta hanyar rashin sanya alamun addini ko aƙida.

Matar wacce abin ya shafa ta shigar da ƙara na ƙalubalantar matakin, inda ta ce an tauye mata ‘yancin yin addininta.

Kasashen Turai sun mayar da hijabi ko gyale da ake sawa a kai da rufe kafadu a matsayin wani batu na nuna wariya a nahiyar a tsawon shakaru.

TRT World