Masu fafutuka na zargin China da kaddamar da gangamin kama wa da daure Musulman Uyghur. Hoto: AA

China ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga babbar malamar Musulunci kuma malamar jami'a bisa tuhumar ta da "barazana ga tsaron kasa", in ji wata kungiyar kare hakkokin dan'adam da ke Amurka.

Masu kare hakkokin dan'adam sun zargi China da kaddamar da gangamin kamawa da daure jama'ar Uyghur, tare da muzanta musu, ana hana su haihuwa da yada al'adunsu wanda wasu jami'an gwamnati da suka hada da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka suka kira da 'kisan kiyashi".

China ta musanta zarge-zargen

A wata sanarwa, Kungiyar Dui Hua ta bayyana cewa Rahile Davut mai shekaru 57 ta yi rashin nasara a daukaka karar da ta yi game da hukuncin farko da aka yanke mata a watan Disamban 2018.

"Wannan ne karo na farko da wani jami'in gwamnatin China ya tabbatar da an yanke hukuncin daurin rai da rai," in ji sanarwar.

Majalisar zartarwa ta China ba ta bayar da amsa game da neman ta ce wani abu da aka yi ba.

Kotunan China na yawan tuhumar mutane da kaso 99.9 inda ba a cika samun kubuta ba a tsarin shari'ar kasar.

Kafin a tsare ta, Rahile Davut, mai shekaru 57, farfesa ce a Jami'ar Xinjiang, kuma mai jagoranci kan nazarin al'adu, yawan jama'a da almarun jama'ar Uyghur.

An kama Davut tun watan Disamban 2017 a arewa maso-yammacin yankin Xinjiang, inda ake zargin Beijing da keta hakkokin dan'adam kan mutane mafi yawan su Musulman Uyghur marasa rinjaye, zargin da take musantawa a koyaushe.

Daraktan Zartarwa na Kungiyar Dui Hua, John Kamm, ya bayyana cewa "wannan yanke hukunci ... bakin zalunci ne, babbar asara ce ga jama'ar Uyghur, da kuma dukkan 'yancin malaman jami'a."

"Ina kira da a sake ta nan da nan don ta dawo zuwa ga iyalanta cikin koshin lafiya."

Davut ta bi sahun masana kuma masu ilimi na jama'ar Uyghur da gwamnatin China ta kama su sama da 300, kuma daga bisani ta kai su kurkuku, wanda hakan na ta faru wa tun 2016, in ji kungiyar.

TRT World