China ta ce ta harba kumbon Long March 2D mai ɗaukar kaya, wanda ya kai tauraron ɗan'adam mai fasahar sansano nesa zuwa sararin samaniya.
An harba kumbon da ƙarfe 7:45 na safe (agogon Beijing) daga cibiyar Ƙaddamar da Kumbo ta Xichang, wadda ke gundumar Sichuan da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Kumbon ya aika da tauraron ɗan'adam mai suna Yaogan-42 02 zuwa samaniya, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua News wanda ke mallakin gwamnati, ranar Lahadi.
Wannan shi ne karo na 17 a shekarar 2024, kuma karo na 517 na harba kumbo ajin Long March, wanda shi ne ƙasar take yawan amfani da shi cikin jerin kumbunanta.
Kumbon samfurin The Long March 2D, yana amfani da makamashi na ruwa ne, kuma yana da ƙarfin ɗagawa da ya kai tan 300. Yana iya safarar kumbon da ke da nauyin tan-1.3 zuwa samaniya da ɗagawar kilomita 700.