A 2011, gwamnatin Hasina ta cire shi daga matsayin shugaban Bankin Grameen, tana mai cewa a shekara 73, ya hauru 60 da ya kamata ya yi ritaya.  / Hoto: AP

Muhammad Yunus da ya taba lashe kambin Laureate, shi ya samar da tsarin bayar da bashi na 'global microcredit movemnent' a Bangaladash, wanda a yanzu ke jagorantar gwamnatin rikon kwaryar kasar, ya kasance babban abokin hamayyar Firaminista Sheikh Hasina wadda ta yi murabus kuma ta gudu ta bar kasar.

An san shi da sunan "bankin talakawa", Yunus da bankin Grameen da ya samar sun lashe kambin 'Nobel Peace Prize' saboda taimaka wa wajen cire miliyoyin mutane daga talauci, ta hanyar ba su basussuka na kasa da dala 100 ga jama'ar karkara da ke fama da talaucin da ba za su iya samun bashi daga manyan bankunan kasar ba.

Mutumin mai ba su bashin kudade ya karfafa gwiwar samar da irin wadannan ayyuka a duniya, ciki har a kasashen da suka ci gaba kamar Amurka inda Yunus ya fara kafa bankin 'Grameen America'.

A yayin da nasararsa ta habaka, Yunus da ke da shekaru 84 a yanzu, ya dan rungumi siyasa inda ya kafa jam'iyyars aa 2007. Amma burinsa na siyasa ya janyo bacin rai ga Hasina, wadda ta zarge shi da 'zukar jinin talaka'.

Masu suka a Bangaladash da suaran kasashe, siki har da India mai makotaka da su, sun ce irin wadannan masu bayar da bashi na karbar riba da yawa don azurta kawunansu daga dukiyar talaka.

Amma Yunus ya ce kudin ruwan da suke karba yana kasa sosai da wanda sauran ankuna ke karba a kasashe masu tasowa, ko kashi 300 ko ma sama da haka da masu bayar da bashi ke nema a wasu wuraren.

Tuhuma sama da sau dari

A 2011, gwamnatin Hasina ta cire shi daga matsayin shugaban Bankin Grameen, tana mai cewa a shekara 73, ya hauru 60 da ya kamata ya yi ritaya.

A watan janairun wannan shekarar, an yanke wa Yunus hukuncin daurin watanni shida a kurkuku saboda karya dokar kwadagi.

A watan Yuni kotun Bangaladash ta kuma zarge shi da wasu mutanen 13 da almundahanar dala miliyan biyu na kudaden walwalar ma'aikatan sadarwa da ya samar.

Duk da cewar ba a daure shi ba, Yunus ya fuskanci tuhuma sama da sau dari bisa zargin cin hanci da rashawa. Yunus ya musanta hannu a dukkan zarge-zargen inda ya kuma ce, zarge-zargen tatsuniyoyi ne kawai.

"Bangaladash ba ta da wata siyasa da ta yi saura," in ji Yunus a watan Yuni, yana sukar Hasina. "Jam'iyya daya tilo kawai ake da ita wadda ta mamaye komai, tana yin komai don cinye zabe ita kadai."

Bayan guduwar Hasina, ya fada wa kafar yada labarai ta India, Times Now Litinin ta zama "ranar 'yanci ta biyu" ga Bangaladash bayan ranar 'yancin kai ta 1971 da kasar ta balle daga Pakistan.

A yanzu haka Yunus na Paris don ganin likita, in ji kakakinsa, yana mai kara da cewar ya yarda da bukatar daliban da suka jagoranci zanga-zangar korar Hasina don zama babban mai bayar da shawara ga gwamnatin rikon kwarya.

Yunus masanin tattalin arziki ne da ya taba koyarwa a jami'ar Chittagong a lokacin da yunwa ta addabi Bangaladash a 1974.

Yunwar da ta yi ajalin dubunnan daruruwan mutane, inda ya dinga fatutukar ganin ta taimaki mutanensa da ke rayuwa a karkara.

TRT World