Hukumar Kula da Yanayi ta Indonesiya ta bayyana cewa girgizar kasar ta afku da misalin karfe 7 da mintuna 50 na safiyar Alhamis din nan a a jihar Java ta Yamma.
A wata dayan da ya gabata kasar da ke Kudu Maso-Gabashin Asiya ta fuskanci motsawar kasa da yawa.
Hukumar nazari kan kasa ta Amurka kuma ta bayyana afkuwar girgizar kasa mai karfin awo 5.5 a yankin Abepurar na kasar Indonesiya.
Jama’ar yankin sun kadu matuka sakamakon afkuwar girzgiar kasar, wadda ta afku a nisa kilomita 22 kudu maso-gabas da garin Sukabumi, kuma a karkashin kasa da zurfin kilomota 104.
Ba a bayar da rahoton samun asarar rayuka ko dukiya ba.
A ranar Talatar da ta gabata ma girgizar kasa mai karfin awo 6.4 ta afku a Indonesiya.
A watan da ya gabata girgizar kasa mai karfin awo 5.6 ta afku a Kudu Maso-Gabashin kasar tare da yin ajalin mutane 321 da lalata gidaje dubu 62,000 a gundumar Ciancur da ke yammacin Java.