MUI tana kira ga  dukkan Musulmai da su nisanci yin mu'amala da amfani da kayayyakin Isra'ila gwargwadon iyawa. Hoto: AFP]

Majalisar Ƙoli ta Malaman Addinin Musulunci ta kasar Indonesiya ta fitar da wata doka a yau Juma’a inda ta bukaci a kaurace wa kayayyaki da kuma ayyuka daga kamfanonin da ke goyon bayan Isra’ila domin nuna goyon bayan Falasdinawa.

Fatawar da Majalisar Malaman Indonesiyan, MUI ta fitar ta ce dole Musulman ƙasar su nuna goyon bayan Falasɗinawa kan "cin zalin da Isra'ila ke musu", a yayin da ta kuma ayyana cewa goyon bayan Isra'ila da masu tallafa mata "haramun ne" ko kuma ya kauce wa dokar Musulunci.

Dokar ta (fatwa) da Majalisar Malamai ta Indonesiya ko MUI ta fitar, ta ce dole ne musulmin kasar su goyi bayan gwagwarmayar Palasdinawa da "zamantakar Isra'ila", tare da bayyana cewa goyon bayan Isra'ila ko magoya bayanta haramun ne, ko kuma adawa da Musulunci.

MUI tana kira ga kowane Musulmi da ya guji yin mu'amala da kuma amfani da kayayyakin Isra'ila gwargwadon iko da kuma waɗanda ke da alaƙa da Isra'ila, da kuma masu goyon bayan mulkin mallaka da aƙidar kafa ƙasar Isra'ila," kamar yadda Asrorun Niam Sholeh, wani jami'in zartarwa na majalisar ya shaida wa manema labarai a ranar Juma'aJuma'a.

"Ba za mu iya goyon bayan ɓangaren da ke yaƙi da Falasɗinu ba, ciki har da yin amfani da kayayyakin da kuɗaɗen da ake samu ta hanyarsu ke tafiya ga tallafa wa kisan gillar da ake yi wa Falasɗinawa."

Isra'ila ta kaddamar da farmaki a Zirin Gaza bayan da Hamas ta kai mata wasu hare-haren ba-zata a kan sansanin sojojinta ranar 7 ga watan Oktoba.

Daga nan ne sai Isra'ila ta ƙaddamar da hare-haren bama-bamai ta sama da ta ƙasa wanda ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce sun kashe mutum fiye da 10,800, galibi fararen hula da yawancinsu ƙananan yara ne.

Duk da cewa a ba faye amfani da fatawowin addini a tsarin gwamnatin Indonesiyan ba, amma suna ƙarfafa wa masu ibada a kasar da ta fi yawan al’ummar Musulmai a duniya ƙwarin gwiwa kan ɗaukar wani mataki.

Indonesiya mai goyon bayan a bai wa Falasdinu ƴancinta na zama ƙasa, ta yi kira da a warware rikicin bisa bin ƙa’idojin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da su, waɗanda suka hada da samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.

AFP