Karin sojojin Isra'ila 23 sun jikkata yayin da rikici ya tsananta a Gaza da Lebanon / Photo: AFP / Photo: Reuters

Litinin, 1 ga watan Oktoban 2024

1347 GMT — Hezbollah ta fafata da sojojin kasa na Isra'ila a garuruwa uku da ke kan iyaka a Lebanon

Mayakan Hezbollah sun gwabza kazamin fada da sojojin kasa na Isra'ila a kan iyakokin kasar guda uku a kudancin kasar Lebanon, kamar yadda kafafen yada labaran kasar Labanon suka bayyana.

Kafar yada labaran ta ce sojojin Isra'ila sun yi luguden wuta kan Aita al-Shaab, Qaouzah da Ramiya da manyan bindigogi.

A gefe guda kuma, wata yarinya 'yar kasar Lebanon ta mutu sakamakon raunukan da ta samu a wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a garin Kharayeb da ke gabashin kasar Lebanon, kamar yadda NNA ta ruwaito.

An kuma bayar da rahoton wasu hare-hare ta sama da dama a garuruwan Kharayeb, Houmine El Faouqa, Jarjouaain, Habbouch da kuma Arab Salim da ke kudancin kasar Lebanon.

1406 GMT — Lebanon ta ce harin da Isra'ila ta kai a babban birnin Baalbek da ke gabashin kasar ya kashe mutum shida ciki har da wani yaro, yayin da kafafen yada labarai na kasar suka rawaito cewa harin ya afka wa wani gini da ke wani yanki mai cike da cunkoso.

"Harin da makiyanmu Isra'ila suka kai...a Baalbek ya kashe mutane shida, ciki har da wani yaro," in ji ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon, kuma kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito cewa dukkan mutanen shida 'yan gida daya ne.

1427 GMT — Karin sojojin Isra'ila 23 sun jikkata yayin da rikici ya tsananta a Gaza da Lebanon

Aƙalla ƙarin sojojin Isra'ila 23 sun sami raunuka a arangamar da aka yi a Gaza da kuma kudancin Lebanon cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Alkaluman sojin Isra'ila sun nuna cewa shida daga cikin sojojin sun jikkata a Gaza, ba tare da bayyana inda sauran sojojin suka jikkata ba.

Alkaluman sun ce akalla sojoji 749 ne aka kashe yayin da wasu 5,018 suka jikkata tun bayan barkewar rikicin Gaza a ranar 7 ga Oktoban 2023.

TRT World