Litinin 28 ga Oktoban 2024
Kungiyar Hezbullah ta ce mayakanta sun kai hari kan sojojin Isra'ila a kudancin Lebanon.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta Hezbollah ta kai hari kan wani sansanin sojojin Isra'ila da ke kusa da kauyen Wazzani da makami mai linzami, bayan sanarwar da ta fitar a baya ta kai hare-hare hudu da rokoki da makaman kan sojojin Isra'ila a Ƙofar Fatima, kan iyakar da aka rufe a kusa da ƙauyen Kfar Kila na Lebanon.
Har ila yau, kungiyar Hezbollah ta bayyana cewa, ta yi wa sojojin Isra'ila kwanton ɓauna a kusa da wani kauye da ke kan iyakar kasar Lebanon tare da harba rokoki kan wani sansanin sojojin ruwa da ke kusa da Haifa na Isra'ila.
A arewacin Gaza, Hamas ta sanar a tashar ta Telegram cewa ta lalata tankin Merkava na Isra'ila da wani bam a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia.
Har ila yau Hamas ta sanar a baya cewa mayakanta sun yi arangama da sojojin Isra'ila a gabashin Jabalia tare da kai hari kan gungun sojoji da makami mai linzami na TBG.
Ƙarin labarai 👇
0812 GMT — Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon, inda ta kashe mutum 20
Akalla ƙarin mutum 20 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon, kamar yadda kafafen yada labarai na Lebanon suka ruwaito.
Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan wani gini a birnin Taya, inda suka kashe mutum uku tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NNA ya ruwaito.
Kafar yada labaran ta ce an kashe karin mutane bakwai da suka hada da ma’aikatan jinya uku tare da jikkata wasu 24 a wani hari da aka kai a garin Ain Baal.
Jiragen yakin sun kuma kai hari kan wani gini a garin Burj al Shamali, inda suka kashe mutum biyar ciki har da ma’aikatan jinya biyu, kamar yadda NNA ta bayyana.
Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta tabbatar da mutuwar mutum 5 tare da jikkata wasu 10 a lokacin da jiragen yakin Isra'ila suka kaddamar da wani sabon hari a unguwar El-Raml da ke birnin Taya.
2237 GMT — Netanyahu na Isra'ila ya ƙi amincewa da shirin Masar na tsagaita wuta a Gaza
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shirin da Masar ta gabatar na tsagaita wuta na wucin-gadi a Gaza da aka yi wa ƙawanya.
Duk da goyon bayan da akasarin ministocin Isra'ila suka yi kan shawarar Masar, Tel Aviv ta yanke shawarar yin watsi da yarjejeniyar ne saboda adawar Netanyahu, wanda ya jaddada cewa "za a yi tattaunawar ne kawai ana cikin yaƙin," a cewar tashar 12 ta Isra'ila.
2116 GMT — Adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Lebanon ya kai 2,672
Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai kan Lebanon tun daga ranar 8 ga watan Oktoban bara ya kai 2,672, tare da jikkata 12,468.
Akalla mutum 19 ne suka mutu yayin da 108 suka jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai a kasar Lebanon a ranar Asabar, a cewar ma'aikatar.
2217 GMT — Al-Qassam ta ce ta kai hari kan motocin sojojin Isra'ila a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia
Rundunar Qassam Brigades, reshen soja na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta sanar da kai hari kan motocin sojin Isra'ila a arewacin Gaza.
A cikin wata sanarwa da suka fitar ta kafar sadarwa ta Telegram sun ce, "Mun auna wani jirgin yakin Yahudawan masu tsaurin ra'ayin kafa ƙasar Isra'ila da wasu buldoza na sojan D9 guda biyu da bama-bamai a kusa da makabartar gabashin Jabalia."
Bugu da ƙari, mayaƙan na Qassam sun kai hari kan tankar Merkava 4 ta Isra'ila tare da bama-baman Shawaz a kusa da tashar Nathr a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia.
2038 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 1,000 a arewacin Gaza cikin makonni uku
Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa sama da 1,000 a arewacin Gaza, tare da tilasta wa rabin al'ummar yankin tserewa daga hare-haren bama-bamai, yayin da sauran rabin suka maƙale ba tare da ruwa ko abinci ba kusan makonni uku, kamar yadda hukumar tsaron farar hula ta Falasdinu ta sanar.
Mahmoud Bassal kakakin hukumar tsaron farar hula ta Falasdinu ya bayyana a cikin wani bidiyo da aka watsa a shafukan sada zumunta cewa sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 1,000 a hare-haren da suka kwashe tsawon makwanni uku suna kai wa a arewacin Gaza, wanda har yanzu ake ci gaba yi.
“Fiye da Falasdinawa 100,000 a yankunan Jabalia da Beit Hanoun, da kuma Beit Lahia na fama da ƙawanya da ruwan bama-bamai da Isra’ila ke yi, yayin da sauran rabin al’ummar da suka kai kusan 200,000, aka tilasta musu yin gudun hijira zuwa birnin Gaza, mafi kusa da gwamnati zuwa arewa,” Bassal ya shaida wa Anadolu.
Ya ci gaba da cewa: Sojojin Isra'ila suna kashe duk wanda ya yi kokarin ba da taimako ga Falasdinawan da suka maƙale a arewacin Zirin Gaza, wadanda ke fama da ƙarancin ruwa da magunguna, da abinci.