WHO ta bukaci a gudanar da bincike a duniya kan cutar X. / Hoto: Getty Images

Bayan da Ebola ta addabi Yammacin Afirka a 2014, wadda ta kama kusan mutane 29,000 tare da yin ajalin sama da 11,000, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta sanar da jerin sunayen cututtukan da za su zama gargadi ga gwamnatoci a yayin da ake tunkarar fadawa annoba.

A 2015, karon farko WHO ta fitar da jerin cututtuka 10 da za a sanyawa idanu', wadanda ta ce suna bukatar a tunkare su cikin gaggawa saboda za su iya zama annoba ko a rasa isassun kayan kula da su a duniya.

Da fari jerin cututtukan sun hada da: Zazzabin Congo Ebola da Marburg da Zazzabin Lass da MERS da SARS Corona da Zazzabin Nipaf da rift.

WHO ta bayyana cewa za a sake yin duba ga jerin sunayen cututtukan a kowacce shekara idan aka samu sabbin cututtuka sun bulla.

A 2018, an kara cutar X a jerin sunayen cututtukan.

Mece ce 'cutar X'?

WHO ta yi amanna da akwai babbar barazana da ba a sani ba (ko aka manta da ita tsawon lokaci) wanda ka iya janyo annoba a fadin duniya a nan gaba.

Tun bayan da aka saka ta a jerin sunayen cututtukan, WHO ta ci gaba da yin gargadi ga shugabannin duniya kan su yi shirin magance X a duk lokacin da ta taso.

WHO ta ware cutar X a matsayin mai illatarwa da ba ta riga ta bayyana cewa "X" na nufin "Wanda ba a tsammanin zuwansa".

Bayan Covid-19, WHO ta bayyana cewar akwai yiwuwar X ce annoba ta gaba mafi muni da za ta afku, "Zai zama abin da ba mu taba gani ba ya ce".

Kai dauki da allurar riga-kafi

Tuni aka fara kiran da a a samar da allurar rigakafin cutar X ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Kamfanonin ere-ere da fasaha na aiki da masanan kimiyya wajen samar da alluran rigakafi ta yadda da zarar an samu barkewar cutar, masana kimiyya za su hada su da kwayoyin halittar da suka dace da su, sannan su samar da riga-kafin.

"Yana da matukar muhimmanci a mayar da hankali ga daukar matakan yaki da cututtuka ta hanyar gudanar da bincike da samun cikakken sakamako. Ba tare da zuba jari a bangaren bincike da samar da magunguna da riga-kafin covid19 ba, da zai yi wahala a iya samar da alluran riga-kafi a kan lokaci," in ji Dr. Michael Ryan, Daraktan Zartarwa na Sashen Gaggawa a WHO.

Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus a wajen Babban Taron Tattalin Arziki na Duniya da aka yi a birnin Davos, ya gargadi shugabannin duniya kan kar su yi watsi da batun X, saboda cuta ce da ba a gama sanin ya take ba.

Ghebreyesus ya ce "Bai kamata mu tunkari matsala ba tare da shiri ba; Za mu iya yin shiri ga abubuwan da ma ba mu san su ba."

Yarjejeniyar annoba

A wajen taron dai, Ghebreyesus ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga shugabannin duniya da su yi aiki da yarjejejniyar Annoba da aka kulla.

Babbar manufar yarjejeniyar da aka kulla ita ce "A karkfafi dukkan gwamnatoci, ail'ummu, karfafafawa kasashe, yankuna a duk duniya wajenyin hakuri da juriya kan wani abu da zai zo a nan gaba."

WHO ta bayyana cewa wannan ya hada da karfafa hadin kan kasa da kasa, sannan a inganta tsarin bayar da gargadi, bayar da bayanai, bincike da adadin jama'arsu, samar da kayayyakin magunguna ga duniya, sai kuma kayan bayar da kariya."

TRT Afrika