Mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta auka wa yammacin Afghanistan sun zarta 2,000 sannan fiye da 10,000 sun jikkata, a cewar kakakin gwamnatin Taliban.
Hukumar kula da yanayi ta Afghanistan ta tabbatar da cewa girgizar kasar, mai karfin maki 6.3 da ta auka wa kasar ranar Asabar, ta kashe mutum 2,053 kawo yanzu. Kazalika ta lalata sama da gida 1,300.
Abdul Wahid Rayan, mai magana da yawun Ma'aikatar Watsa Labarai da Al'adu, ya ce mutanen da suka mutu a yankin Herat sun zarta adadin da aka bayyana da farko.
Ya ce girgizar kasar ta lalata kusan kauyuka shida, kuma gine-gine sun danne daruruwan mutane, yana mai yin kira a kai musu agajin gaggawa.
Sai dai kamfanin dillancin labaran kasar Bakhtar News Agency, ya ambato hukumar bayar da agaji ta Afghan Red Cresent tana cewa kauyuka 12 da ke yankunan Zinda Jan Ghorian na lardin Herat – inda kusan mutum miliyan 1.9 ke zaune – sun lalace "baki daya."
Masu aikin agaji suna can suna kokarin zaro matattu da wadanda ke da sauran numfashi daga baraguzan gine-ginen da suka danne su.