Emmanuel Macron ya goyi bayan Ministan Ilimi kan haramta sanya abaya / Hoto: Reuters

Shugaban Faransa ranar Juma'a ya ce gwamnatinsa ba za ta fasa aniyarta ta haramta sanya abaya a makarantu ba.

Emmanuel Macron ya ziyarci wata makarantar sakandare a garin Orange da ke kudancin Faransa, inda ya yi tsokaci game da haramta sanya abaya da kasar ta yi.

"Makarantun kasarmu babu ruwansu da addini, kuma karatu kyauta ne sannan dole ne … duk wata alamar addini ba ta da gurbi (a nan)," in ji Macron, a cewar gidan talabijin na BFMTV.

Shugaban kasar ya goyi bayan matsayin da Ministan Ilimi Gabriel Attal ya dauka, yana mai cewa: "Ba za mu sauya wannan matsayi ba ... Za mu tabbatar mun aiwatar da shirin."

Labari mai alaka: Za a haramta wa mata sanya abaya a makarantun Faransa

Macron ya ce za a tura ma'aikata don goyon bayan shugabannin makarantun da ake fuskantar kalubale wajen aiwatar da dokar, sannan za a kafa wani kwamiti na tattaunawa da dalibai da iyayensu. "Ba za mu bar komai ya wuce ba tare da daukar mataki ba," in ji shugaban kasar.

Attal ya sanar cewa daga ranar Litinin ba za a bari daliban da ke sanya abaya su shiga aji ba, lokacin da za a dawo daga hutu.

"Za mu yi wa dalibai maraba da dawowa makaranta kuma za a tattauna domin fahimtar da su dalilan yin wannan doka da kuma abin da ya sa ba za mu bari a rika sanya abaya a makarantu ba," a cewar Attal.

Gwamnatin Faransa tana shan suka bisa yi dokokin musguna wa Musulmai ciki har da dokar kai samame masallatai da cibiyoyin Musulunci.

AA