Sakataren tsaro na Amurka Lloyd Austin ya ce Washington ba ta neman sansani na dindindin a kasar Papua New Guinea (PNG), da ke Tsibiran Pacific a karkashin sabuwar yarjejeniyar tsaro da aka cimma.
Austin ya fadi hakan ne a ranar Alhamis yayin wata tattaunawa da Firaministan Papua New Guinea James Marape, a wata ziyara da ya kai don inganta dangantakar tsaro a tsakaninsu.
Papua New Guinea da Amurka sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar hadin kai kan tsaro a watan Mayu, wacce za ta bai wa Amurka damar farfado da tasoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama na PNG don amfanin sojoji da fararen hula.
Daftarin yarjejeniyar ta nuna cewa za a bar dakarun Amurka da kayan aikinsu a Papua New Guinea, tare da kula da sansanin rundunar sojin ruwa na Lombrum wanda Australia da Amurka ne suka gina shi.
Sai dai har yanzu majalisar dokokin Papua New Guinea ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba.
"Ina so na yi bayani sosai cewa, ba neman kafa sansani na dindindin muke yi ba a Papua New Guinea," kamar yadda Austin ya shaida wa taron manema labarai a babban birnin PNG Port Moresby.
Ya ce kasashen biyu suna karfafa alakar da dama take tsakaninsu ne, kuma za su zamanantar da dakarun tsaron Papua New Guinea.
Kokarin hana shiri da China
Amurka da kawayenta na kokarin ganin sun raba kasashen da ke tsibirin Pacific yin duk wata alakar tsaro da China, a yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan batun Taiwan, bayan da Beijing ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsaro da kasar Solomon Islands.
"Hadin kan tsaron ba don komai ba ne sai don Amurka ta inganta karfin PNG a fannin soja amma ba hadin kan shirin yaki ba ne," kamar yadda shi ma Firaminista Marape ya fada a ranar Alhamis din.
Ya kara da cewa "Amurka ba ta bukatar PNG wajen kaddamar da duk wani yaki a ko ina a duniya."
"Suna da sansanai a Philippines da Koriya ta kudu da ma wasu wuraren da suka fi kusa da China," ya ce.