Australia ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da za ta ba da damar musayar sirrin nukiliya da kayan aiki da Amurka da Birtaniya.
Yarjejeniya, a cewar Australia wani muhimmin mataki ne da zai samarwa sojojin ruwanta da jiragen karkashin ruwa masu amfani da makamashin nulikya kayan aiki.
Yarjejeniyar ta haɗa kasashen uku a fannin tsare-tsaren tsaro ta hanyar isar da muhimman bayanan nukiliyar Amurka da Birtaniya da kuma ƙwarewarsu a matsayin wani bangare na yarjejeniyar AUKUS ta 2021 kan tsaron kasashe ukun.
Yarjejeniyar ta AUKUS, wadda ta kuɗuri aniyar kera jiragen karkashin ruwa na Austrialia mai amfani da makamashin nukiliya tare da haɗa gwiwa wajen ɓunkasa hanyoyin yaki, wata dabara ce ga martani ga ƙuɗurin sojojin China a yankin Pacific.
"Wannan yarjejeniya, wani muhimmin mataki ne ga Australiya a ƙuɗurinta na mallakar jiragen ruwa masu amfani da makamashin nukiliya ga rundunar sojojinta na ruwa," a cewar ministan tsaro kuma mataimakin Firaministan Australiya, Richard Marles.
Shirin mallakar jirgin ruwa mai amfani da makamashin nukiliyar da Australiya ta sa a gaba za kafa "mafi girman hanyoyi hana yaduwar makaman nukiliya", in ji shi, yana mai jaddada cewa ƙasar ba ta buƙatar makaman nukiliya.
Muhimmacin jiragen karkashin ruwa
Yarjejeniyar baya-bayan nan wacce aka sanya wa hannu a birnin Washington a makon jiya sannan aka gabatar da ita a gaban majalisar dokokin Australiya, ta bai wa ƙasar damar ladabtar da abokan huldarta a duk wani abu da ka iya janyo barazana a yarjejeniyar nulikiyar daga kayan aikin da aika zuwa ƙasar.
Za a tura makaman nukiliyar jiragen karkashin ruwa daga Amurka ko Birtaniya a ''cikakkiyar na'urar samar da wutar lantarki'', a cewar yarjejeniyar.
Ko da yake dai Australiya za ta ɗauki alhakin adanawa da zubar da man nukiliya da sauran dattin da ke cikin rukunin makamashin nukiliyan wadanda aka sanya karkashin yarjejeniyar.
''Jiragen ƙarkashin ruwan wasu muhimman bangare ne na karfin sojan Australiya, inda suke samar da dabaru ta fuksan bayanan sirri da kare hanyoyin tekunmu,'' in ji yarjeniniyar.
Ministan Harkokin Wajen China, Wang Yi ya yi wani gargadi a wata ziyara da ya kai Australiya a watan Afrilu da cewa, yarjejeniyar AUKUS ta tada ''mumunan haɗarin yada makaman nukiliya,'' yana mai cewa jhakan ya sabawa yarjejeniyar Kudancin Pacific wadda ta haramta makaman nukiliya a yankin.