Ko a ranar Asabar sai da Kungiyar Palestinian Red Crescent ta ce asibitin tankokin yakin Isra'ila kusan 20 na daf da asibitin na Al-Quds. Hoto/AA

'1625 GMT — Yan sanda sun ce kusan mutum 45,000 sun fito zanga-zanga a Australia

Dubban mutane ne a ranar Lahadi suka taru a Australia inda suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza.

Masu zanga-zangar sun taru a gaban State Library of Victoria da ke Melbourne kafin suka nufi majalisar kasar.

Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a fadin duniya. Hoto/Getty Images

‘Yan sanda sun bayyana cewa kusan mutum 45,000 suka halarci zanga-zangar inda masu zanga-zangar suka rinka kira kan a kawo karshen kawanyar da aka yi wa Gaza da kuma tsagaita wuta.

1425 GMT — Zuwa Alhamis duka hanyoyin sadarwa a Gaza za su katse

Ministan Sadarwa na Falasdinu Yitzhak Sidr a ranar Lahadi ya sanar da cewa zuwa ranar Alhamis mai zuwa hanyoyin sadarwa baki daya za su katse a Zirin Gaza saboda karancin fetur.

Ya bayyana haka ne a lokacin taron manema labarai inda ya ce wannan katsewar za ta shafi kungiyoyin bayar da agaji da dama da ke aiki a Gaza.

Zuwa yanzu Falasdinawa 11,11 aka kashea Gaza, daga ciki har da yara 4,406 da mata 3,027.

1300 GMT — Kungiyar Palestinian Red Crescent ta ce asibitin Al-Quds ya daina aiki

Kungiyar bayar da agaji ta Palestinian Red Crescent a ranar Lahadi ta sanar da cewa Asibitin Al-Quds da ke Gaza ya daina aiki saboda karancin man fetur da kuma rashin wuta.

Haka kuma kungiyar ta tabbatar da cewa ta kasa tuntubar duka wadanda ta sani da ke a asbitin na Al-Quds.

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar da cewa ta rasa hanyoyin sadarwa tsakaninta da cibiyarta da ke Asibitin Al-Shifa da ke Gaza.

1015 GMT — Ministan Tsaron Isra'ila na da'awar a 'kawar' da duk wani mai goyon bayan Hamas

Ministan Tsaron Isra’ila mai ra’ayin rikau Itamar Ben-Gvir ya yi da’awar cewa a kawar da duk wani mai goyon bayan Hamas.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da tashar Isra’ila ta Channel 12 inda ya ce “A bayyane yake idan suka ce ana bukatar kawar da Hamas, hakan na nufin masu waka da masu goyon baya da masu rarraba alewa, duk wadannan ‘yan ta’adda ne.”

Ben-Gvir, wanda a baya-bayan nan ya fito fili tare da raba makamai ga fararen hula a duk fadin Isra'ila da kuma Yahudawa mazauna yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan, ya shahara da ra'ayinsa na kishin Yahudawa.

0940 GMT — Sojojin Isra'ila sun kara kashe wani matashi a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Sojojin Isra’ila sun kara kashe wani Bafalasdine a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Lahadi, lamarin da ya ja adadin Falasdinawan da aka kashe a gabar ya kai 186, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta tabbatar.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce “Sojojin Isra’ila sun harbe Montaser Muhammad Amin Saif mai shekara 34 a ranar Lahadi a kauyen Burqa da ke arewacin Nablus.”

Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ce sojojin sun shiga kauyen na Burqa inda suka yi bincike a gidaje da dama.

0910 GMT — WHO ta ce ta kasa tuntubar asibitin Al-Shifa na Gaza saboda yanke hanyoyin sadarwa

Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus a safiyar Lahadi ya tabbatar da cewa babu wata hanya da kungiyarsa ta WHO za ta tuntubi asibitin Al-Shifa da ke Zirin Gaza.

“WHO ta rasa hanyoyin sadarwa tsakaninta da cibiyarta da ke Asibitin Al-Shifa da ke Gaza, a daidai lokacin da ake samun rahotanni masu ban tsoro na karin hare-hare,” kamar yadda Tedros ya bayyana a shafin X.

Mista Tedros ya bayyana cewa wasu rahotanni sun ce wasu da suka gudu daga asibitin an harbe su inda aka kashe su, wasu kuma an ji musu rauni.

AA
AFP
Reuters
AP
TRT World