Sheikh Ekrima Sabri, babban limamin Masallacin Ƙudus, ya yaba wa Falasdinawa muminai kan shiga masallacin duk da takunkuman Isra'ila. / Hoto: Reuters / Photo: AFP

14:00 GMT— Ɗaruruwan Falasɗinawa sun bijire wa hanin Isra'ila na shiga Masallacin Ƙudus a Juma'ar farko ta Ramadan

Duk da takunkumin da Isra'ila ta saka, dubban Falasdinawa daga yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye sun samu damar shiga Masallacin Ƙudus da ke Gabashin Birnin Ƙudus a ranar Juma'a ta farko ta watan Ramadan, don gabatar da sallarsu ta mako-mako a cikin jam'i yayin da suke azumi.

"Musuulmai kusan 80,000 ne suka yi Sallar Juma'a a Masallacin Ƙudus," in ji Ma'aikatar Kula da Harkokin Musulunci a Birnin Ƙudus a cikin wata sanarwa.

Sheikh Ekrima Sabri, babban limamin Masallacin Ƙudus, ya yaba wa Falasdinawa muminai kan shiga masallacin duk da takunkuman Isra'ila.

“Kwarararku mai albarka tana isar da saƙo ga masu kwaɗayin shiga masallacin cewa ba ruwansa da rarrabuwar kawuna kuma na Musulmai ne kawai, babu inda za a yi sulhu ko a bar wani ɓangare nasa,” ya shaida wa masallatan.

Sabri ya bukaci al’ummar Musulmi da su zo Masallacin Ƙudus, yana mai cewa, “Idan aka hana su, za su iya yin salla a inda ta riske su, tare da fatan samun ladan yin salla a Masallacin Ƙudus.

0800 GMT — Masar na neman a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza: Sisi

Shugaba Abdel Fattah el Sisi ya ce Masar na neman a tsagaita wuta a Gaza, da ƙara shigar da kayan agaji, da ba da damar 'yan gudun hijira a kudancin yankin su koma arewacin kasar.

Masar na neman a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza: Sisi / Hoto: Reuters

Sisi, wanda ke magana a cikin wani saƙon faifan bidiyo, ya kuma yi gargadi game da haɗarin kutsen da Isra'ila ke da shi a garin Rafah da ke kan iyaka.

0600 GMT — Hamas ta gabatar da shirin tsagaita a Gaza, ta mayar da hankali wurin musayar fursunoni

Ƙungiyar Hamas ta gabatar da shirin tsagaita wuta a Gaza ga masu shiga tsakani inda matakin farko zai haɗa da sakin matan Isra'ila da ƙananan yara da tsofaffi da marasa lafiya cikin waɗanda ta yi garkuwa da su, yayin da ita kuma za a sakar mata fursunoni Falasɗinawa 700 zuwa 1000, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana, yana mai ambato takardar da ƙungiyar ta tsara game da batun

Cikin waɗanda ƙungiyar take so a saka har da fursunoni Falasɗinawa guda 100 da Isra'ila ta yi wa ɗaurin rai-da-rai da kuma "mata da Isra'ila ta ɗauka aiki."

Hamas ta ce za ta amince game da batun daina buɗe wuta na dindindin bayan an aiwatar da wannan shirin da ta gabatar, a cewar bayanan da ke cikin takardar.

Kazalika ta ce za a ƙulla yarjejeniya kan tsayar da ranar da Isra'ila za ta janye daga Gaza duka bayan wannan mataki na farko.

Ƙungiyar wacce ke gwagwarmayar kare hakkin Falasɗinawa ta ce za a saki mutanen da ake tsare da su na dukkan ɓangarorin biyu a mataki na biyu na yarjejeniyar da ta gabatar.

2200 GMT — Isra'ila ta kashe tare da jikkata mutane da 'dama' da ke jiran agajin abinci a Gaza

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta ce Isra'ila ta kai hari kan Falasdinawa da ke jiran agajin jinƙai a zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, lamarin da ya yi sanadiyar kashe tare da jikkata wasu da dama.

Ta kuma ƙara da cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa yayin da aka kai gawarwaki akalla 21 da wasu fiye da 155 da suka jikkata zuwa asibitoci.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce Falasɗinawa na jiran agajin jinƙai a mashigin Gaza na Kuwaiti, inda ta ce tana nuna shirin da Isra'ila ta yi na aiwatar da wani sabon kisan kiyashi mai ban tsoro.

Hukumar ta ce ana ci gaba da aikin kwashe wadanda suka mutu da waɗanda suka jikkata duk da ƙalubalen da yankin ke fuskanta.

Sanarwar ta ƙara da cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa saboda mummunan yanayin da waɗanda suka jikkata ke ciki, waɗanda ake kula da su a asibitocin da ke kusa.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Falasɗinu WAFA ya tabbatar da cewa an kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.

Sojojin Isra'ila kamar yadda suka saba sun nisantar da kansu daga sabon kisan gillar na Gaza, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce sojojinta da suka mamaye yankin ba su yi luguden wuta kan Falasɗinawa da ke jiran agaji ba.

Mohammed Ghurab, daraktan bayar da agajin gaggawa a wani asibiti a arewacin Gaza, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, sojojin sun buɗe wuta kai-tsaye a kan mutanen da suka taru a zagayen dajin domin jiran wata motar abinci.

Wani ɗan jarida na AFP da ke wurin ya ga gawawwaki da kuma mutanen da aka harbe.

Wani dan jarida na AFP da ke wurin ya ga gawarwaki da kuma mutanen da aka harbe. / Photo: AA

2143 GMT — Ofishin Netanyahu ya ce sabon matakin sasantawa da Hamas har yanzu ba shi da tabbas

Ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce wata sabuwar shawara da ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta gabatar ga masu shiga tsakani ba ta kan tsarin da ya dace.

Sanarwar ta ce a ranar Juma'a za a gabatar da cikakken bayani kan batun ga majalisar ministocin yaƙin da tsawaita wa'adin tsaro.

TRT Afrika da abokan hulda