A bara ne, gwamnatin Birtaniya ta sanar da wani sabon shiri mai cike da ce-ce-ku-ce, da ya ba da damar a tura masu neman mafaka a kasar zuwa Rwanda domin a tsugunar da su a can. / Hoto: AP

Mazauna Birtaniya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da shirin gwamnatin kasar na yaki da bakin-haure da kuma kalaman jami'an gwamnati na hana kaura zuwa kasar.

Jama'a ne suka taru a ranar Litinin a gaban majalisar dokokin Birtaniya domin nuna adawa da manufofin gwamnati na kaura a wani gangami da kungiyar da ke yaki da nuna wariyar launin fata ta ‘Stop Racism platform’, da kungiyar ilimi ta kasa da kuma kungiyar ma'aikatan gwamnati da ‘yan kasuwa (PCS) da kuma dandalin Care 4 Calais suka shirya.

Bell Ribeiro-Addy, 'yar majalisar dokoki ta jam'iyyar adawa ta Labour, kana ministar kula da shige da fice ta kasar, ta soki shirin gwamnati na korar bakin haure ba bisa ka'ida ba zuwa Rwanda tare da dokar shige da fice ba bisa ka'ida ba.

Shirin Birtaniya kan Rwanda da yakin da take yi na masu kaura ba mai “yiwuwa ba ne sannan kuskure ne kuma ya saba wa dokokin kasa da kasa,” a cewar Ribeiro-Addy.

Ta kara da cewa al’ummar Birtaniya ba su amince da wannan shiri na gwamnati ba.

Ta ce wasu daga cikin masu neman mafaka a Birtaniya na bukatar a ba su kariya sosai, tana mai cewa kamfanoni da dama suna samun kudi mai yawa albarkacin bakin haure da ke kasar.

"Hakki ne da ya rataya a wuyanmu mu bude kafofinmu ga bakin-haure," in ji Bell.

An gabatar da kudirin dokar gwamnati kan shige da fice a farkon watan nan domin kama bakin-haure da ke shiga kasar cikin kwale-kwale.

Dokar za ta bayar da dama tsare mutanen da suka isa kasar cikin kananan kwale-kwale har tsawon kwanaki 28 ba tare da beli ko saurarar korafinsu ba.

A shekarar da ta gabata, gwamnatin Birtaniya ta sanar da wani sabon shiri mai cike da ce-ce-ku-ce, wanda ya ba da damar a tura duk masu neman mafaka da ke yunkurin shiga Birtaniya zuwa Rwanda domin a tsugunar da su a can.

TRT World