Kafofin watsa labaran Iran sun ce gwamnatin kasar ta soma aiki da kyamara domin gano matan da ba sa sanya hijabi sannan a tursasa musu yin hakan.
A makon jiya ne aka sanar da shirin soma aiki da kyamarar da zummar "tilasta bin dokar" sanya hijabi lamarin da ya jawo suka da zanga-zanga daga wasu bangarori.
Ranar Juma'a sabon babban sufeton 'yan sandan kasar Ahmed-Reza Radan, ya jaddada cewa za a tursasa sanya hijabi ta hanyar yin amfani da kyamarori don gano matan da ba sa sanyawa "ba tare da yin kura-kura ba."
Ya yi tsokacin ne bayan tambayoyin da aka yi game da yiwuwar kyamarori su yi kuskure wajen gano matan da ba su sanya hijabi daidai ba.
Kazalika za a hukunta mutanen da ke karfafa gwiwar mata su cire hijabansu, kuma ba za a ba su damar daukaka kara ba, in ji mataimakin antoni janar na Iran, a cewar kafofin watsa labaran kasar.
Za a sanya kyamarorin ne a wuraren hada-hadar jama'a domin gano matan da ke "karya dokokin" sanya hijabi, a cewar wata sanara da 'yan sanda suka fitar.
A kwanakin baya fitattun mata 'yan fim da masu fafutika sun rika sanya hotunansu ba tare da hijabi ba a soshiyal midiya don bijire wa wannan doka.