Dakarun tsaron gabar tekun Turkiyya sun kubutar da bakin-haure 69 a wani aikin agaji da suka gudanar a tekun Aegean bayan korar su da hukumomin kasar Girka suka yi zuwa yankin tekun Turkiyyar.
Rundunar tsaron gabar tekun Turkiyya a yankin Arewacin Aegean ta ce ta ceto bakin-haure 45 daga cikin wani jirgin ruwa a gabar tekun Ayvacik na lardin Canakkale a ranar Litinin.
Bakin-hauren dai sun fito ne daga Afghanistan.
A wani lamari na daban da ya faru a ranar Lahadi, rundunar ta bayyana cewa ta ceto wani kwale-kwale da ake hura wa iska dauke da bakin-haure 24 wadanda ke tafe ba bisa ka'ida a gabar tekun lardin Izmir.
Kuma tuni aka aika da wani jirgin ruwa na masu gadin gabar tekun zuwa yankin bayan samun labarin cewa akwai wasu 'yan ci-rani da ke makale cikin kwale-kwale da ke kusa da gundumar Dikili ta Izmir a cewar jami’ai.
An mika bakin-hauren da aka gano a Canakkale da Izmir ga Hukumar Kula da Shige da Fice ta lardin.
Turkiyya da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun sha yin Allah wadai da irin haramtaccen matakin da Girka ke dauka na korar masu neman mafaka,
Sun ce hakan ya saba wa ka'idojin jinkai da kuma dokokin kasashen kuma yana jefa rayuwar bakin-haure masu rauni, da suka hada da mata da kananan yara, cikin hatsari.
Turkiyya dai ta kasance wata muhimmiyar hanyar wucewa ga 'yan gudun hijira da bakin-haure da ke son tsallakawa zuwa Turai don fara sabuwar rayuwa, musamman wadanda ke guje wa yaki da tsanantawa.