Hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kai wa a Gaza sun kashe 'yan jarida goma sha daya, sun jikkata fiye da 20 sannan 'yan jarida biyu sun bata, a cewar wata kungiyar Falasdinawa 'yan jarida a sabon rahoton da ta fitar.
A cewar rahoton da kungiyar Freedom Committee, wadda ke da alaka da kungiyar Falasdinawa 'yan jarida ta fitar ranar Lahadi, an tabbatar da mutuwar Falasdinawa 'yan jarida 11 a harin da Isra'ila ta kaddamar ranar 7 ga watan Oktoba.
Kungiyar ta ce da gangan Isra'ila ta kai hare-hare kan 'yan jaridar da "aka kashe" a hare-haren da ta kai a Gaza har zuwa ranar 15 ga watan Oktoba. Ta koka kan yadda "aka samu karuwar kai hare-hare kan Falasdinawa 'yan jarida."
Rahoton ya kara da cewa jiragen yakin Isra'ila sun rika yin luguden wuta a gidajen 'yan jarida da dama, bayan tun da farko sun sanar da kai hare-hare kan gidajen 'yan jarida 20.
An lalata ofisoshin gidajen kafafen watsa labarai
Kazalika Isra'ila ta lalata ofisoshi da hedikwatar akalla kafafen watsa labarai 50 wadanda suka hada da Al Aqsa Media Network, Ma'an News Agency, Al Quds newspaper, Baladna Radio, Zaman Radio, Al Quran Radio, ofishin Al Jazeera, Palestine TV, da ofisoshin kamfanin dillancin labarai na AFP, a cewar rahoton.
Rahoton ya kara da cewa a Gabar Yammacin Kogin Jordan, Isra'ila ta jikkata Falasdinawa 'yan jarida da dama, ta ci zarafin wasu, ta daure wasu, ta hana wasu gudanar da ayyukansu, ta kwace kayan aikin da dama daga cikinsu sanna ta lalata kayana aikin.
Haka kuma Isra'ila ta rika katse hanyoyin sanarwar kafafen watsa labarai, in ji rahoton. Ya ce: "Gidan talbijin na Al Aqsa ya daina watsa labarai ta hanyar tauraron dan'adam na Eutelsat saboda kutsen da aka rika yi masa."