An gano wani babban kabari a Asibitin Al Shifa da ke Gaza, a cewar wani rahoton Al Jazeera Arabic. Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da Rundunar Ƴan-kato-da-gora ne suka gano kabarin.
Gidan talbijin ɗin da ke ƙasar Qatar ya ce an tono gawawwaki tara ranar Litinin a wajen asibitin da ke yammacin Gaza, sai dai jami'an kiwo lafiya sun dakatar da ci gaba da tono gawawwakin saboda fargabar da suke yi kan yiwuwar fuskantar hari daga jirage marasa matuƙa na Isra'ila da ke shawagi a yankin.
Gawawwakin da aka tono, waɗanda ba su gama ruɓewa ba, sun nuna cewa dakarun Isra'ila ba su jima da "kashe" mutanen ba, kuma alamu sun nuna cewa wasunsu marasa lafiya ne domin kuwa akwai bandeji a jikinsu, a cewar rahoton.
Dangin wasu daga cikin mutanen da aka tono gawawwakinsu sun gane ƴan'uwansu cikinsu har da wani dattijo da wata mace da kuma wani matashi ɗan kimanin shekara 20.
Ma'aikatan asibitin da likitoci sun bayyana cewa an kashe mutane da dama a wajen babbar ƙofar shiga asibitin, wadda ake kira ƙofa mai lamba 80. Kazalika ma'aikatan lafiya sun ce sun ga lokacin da dakarun Isra'ila suka kashe wasu mutanen.
A kwanakin baya ne dakarun Isra'ila suka janye daga Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza bayan sun kwashe mako biyu suna mamaye shi, kuma sun ce sun yi ba-ta-kashi da mayaƙan Hamas a cikin asibitin da a baya ake kallo a matsayin babbar cibiyar kiwon lafiya ta Falasɗinawa.
Ganau sun ce sojojin Isra'ila sun kashe tare da jikkata mutane da dama kafin su janye daga asibitin. Haka kuma sun lalata ginin asibitin da gine-gine da ke maƙwabtaka da shi.
Kazalika sojojin Isra'ila sun lalata sashen da ake kula da masu fama da cutar ƙoda da sashen da ake karbar haihuwa da mutuware da wuraren da ake kula da masu cutar kansa da waɗanda suke fama da ƙuna, in ji shaidu.
A cewar wasu majiyoyin ma'aikatar kiwon lafiya ta Falasɗinu, yanzu asibitin ba ya aiki kwata-kwata kuma sojojin Isra'ila sun lalata dukkan nau'urorin asibitin.