Hajjin bana na cikin wanda aka fi fuskantar tsananin zafi a tarihi. / Hoto: AFP

Hukumomi a Saudiyya sun ce alhazai sama da 1,300 ne suka mutu lokacin Hajjin bana wanda aka gudanar a yanayi na tsananin zafi, kuma yawancin waɗanda suka mutu ba su da takarda ta izinin yin aikin na Hajji.

"Abin takaici shi ne, mutanen da suka mutu sun kai 1,301, kuma kashi 83 daga cikinsu sun zo aikin Hajji ne ba tare da izini ba inda suka yi tafiyar-ƙafa mai tsawo cikin tsananin zafin rana, ba tare da makwanci ko kulawa ba," in ji wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Saudiyya Saudi Press Agency ya bayar ranar Lahadi.

Wasu bayanai da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara a makon jiya, bisa ƙididdigar da hukumomi suka yi da kuma alƙaluma daga jami'an diflomasiyya na ƙasashen da suka tura jama'arsu Hajji, sun nuna cewa alhazan da suka mutu sun kai 1,100.

Alhazan da suka rasu sun fito ne daga ƙasashe fiye da 10 daga Amurka zuwa Indonesia, kuma wasu gwamnatoci suna ci gaba da sabunta alƙaluman 'yan ƙasashensu da suka rasu.

Jami'an diflomasiyya na ƙasashen Larabawa sun shaida wa AFP a makon jiya cewa 'yan ƙasar Masar guda 658 ne suka mutu — kuma 630 daga cikinsu ba su yi rajistar aikin Hajji ba.

Jami'an na diflomasiyya sun ce yawancin mutanen sun rasu ne sakamakon tsananin zafi.

A wasu lokutan, yanayin zafi a Makkah ya kai digiri 51.8 a ma'aunin salshiyos, a cewar hukumar kula da yanayi ta Saudiyya.

Hukumomi a Riyadh ba su ce komai ba game da waɗannan alƙaluma na alhazan da suka mutu har sai ranar Lahadi.

Sai dai, ranar Juma'a wani babban jami'in gwamnatin Saudiyya ya shaida wa AFP cewa alƙaluman wucin gadi sun nuna cewa alhazai 577 ne suka mutu a ranaku biyu na ƙololuwar aikin Hajji: ranar 15 ga watan Yuni, da aka yi Tsayuwar Arafat, da kuma ranar 16 ga watan Yuni, lokacin da aka yi jifan Shaiɗan a Mina.

Ministan Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya, Fahd al Jalajel, ranar Lahadi, ya bayyana Hajjin bana a matsayin wanda ya yi "nasara", kamar yadda SPA ya ruwaito.

Ya ce ma'aikatar lafiya ta "kula da lafiyar fiye da mutum 465,000, cikinsu har da mutum 141,000 da ba su da takardar izinin aikin Hajji."

Hukumomin Saudiyya sun ce mutum fiye da miliyan 1.8 suna gudanar da Hajjin bana, kamar adadin waɗanda suka yi Hajji a bara, suna masu cewa mahajjata miliyan 1.6 sun je ne daga ƙasashen waje.

AFP