Ziyarar Shugaban Turkiyya Erdogan zuwa Indonesia ta mayar da hankali ne kan tattalin arziƙi da haɗin kan yanki. / Hoto: AA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Indonesia Prabowo Subianto a ranar Laraba inda suka tattauna da nufin karfafa alakar tattalin arziki da tsaro a tsakanin kasashen biyu masu rinjayen musulmi.

Kasashen biyu na gudanar da taronsu na farko na kwamitin manyan tsare-tsare na haɗin gwiwa bayan amincewa da kafa kwamitin a wani taro a Bali a shekarar 2022.

"Wannan taron shi ne taro mafi girma tsakanin kasashen biyu, inda za a tattauna dukkan batutuwan da suka amfanar juna, da suka hada da muhimman batutuwa," in ji Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Indonesiya Rolliansyah Soemirat.

Sanarwar da Turkiyya ta fitar ta ce tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi yanki da duniya musamman yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza.

A ranar Litinin shugaban na Turkiyya ya gana da Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim inda ya jaddada rashin amincewarsa da shawarar Amurka na mayar da Falasdinawa daga Gaza inda ya ce kamata ya yi Isra'ila ta biya kudin sake gina yankin.

"Ba mu dauki shawarar korar Falasdinawa daga kasashen da suka shafe shekaru dubbai a matsayin wani abu da za a dauka da muhimmanci ba," in ji Erdogan.

"Ba mu ɗauki shawarar da aka bayar ba ta korar Falasɗinawa daga ƙasarsu da suke zaune tsawon dubban shekaru da muhimmanci ba," in ji Erdogan.

TRT World