Erdogan ya jaddada cewa: "Mun tsaya tare da 'yan'uwanmu Falasɗinawa ta kowace fuska, musamman a lokacin da ake cikin mawuyacin hali, mun tattara dukkanin albarkatunmu ga Falasɗinu, ga al'ummar Gaza da ake zalunta." / Hoto: AA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da Isra'ila ke kai wa Falasɗinawa a Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, inda ya bayyana waɗannan ayyuka a matsayin tabo maras gogewa a tarihin ɗan'adam.

Isra’ila na aiwatar da wadannan kisan kiyashi tare da goyon bayan Ƙasashen Yammacin Duniya, kamar yadda Erdogan ya shaida wa taron kungiyar Jam’iyyar Adalci da Ci Gaba a Majalisar Dokokin Turkiyya a jiya Laraba.

Da yake jaddada cewa sojojin Isra'ila sun kashe sama da yara 14,000 da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba, Erdogan ya yi furucin cewa zaluncin Tel Aviv ya zarce na ƴan Nazin Jamus da shugabanta Adolf Hitler.

Erdogan ya ce, babu wanda zai iya ƙalubalantar yadda Turkiyya ke ji kan batun Falasɗinu, ya ƙara da cewa lamarin Falasɗinu ya bai wa rayuwarsa sabuwar ma'ana.

"Matuƙar Allah ya ba ni tsawon rai, zan ci gaba da kare gwagwarmayar Falasɗinu, kuma zan kasance muryar al'ummar Falasɗinawa da ake zalunta," in ji shi.

Shugaban ya tuna da shekaru 15 da suka gabata, a taron tattalin arzikin duniya na 2009 a Davos, Switzerland, lokacin da ya ƙalubalanci shugabancin Isra'ila da zaluncin da suke yi wa Falasɗinawa, a wata ganawa da ta yi ƙamari, ta hanyar nuna rashin amincewa da "minti daya!"

"Lokacin da babu wanda zai yi magana, sai muka miƙe muka ce: Hamas ba kungiyar ta'addanci ba ce, amma kungiyar gwagwarmaya." Mun gabatar da taswirori a Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna yadda Isra’ila ta mamaye yankunan Falasdinu a hankali a cikin shekaru 70 da suka gabata,” in ji shi.

Erdogan ya jaddada cewa: "Mun tsaya tare da 'yan'uwanmu Falasdinawa ta kowace fuska, musamman a lokacin da ake cikin mawuyacin hali, mun tattara dukkanin albarkatunmu ga Falasdinu, ga al'ummar Gaza da ake zalunta."

Ya sake nanata ƙudurin Turkiyya na jajircewa wajen kare fafutukar neman 'yancin kai na Falasɗinu a kowane hali.

Haniya zai ziyarci Turkiyya

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da Ismail Haniya shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas sun gana a birnin Doha a ranar Laraba inda suka tattauna kan batun Gaza, a cewar majiyoyin diflomasiyya.

Majiyar ta ƙara da cewa, Fidan ya gana da Haniya da tawagarsa, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi taimakon jinƙai a Gaza datsagaita wuta, da kuma wadanda aka yi garkuwa da su.

A cewar sanarwar da Erdogan ya fitar, Haniya na shirin kai ziyara Turkiyya a karshen mako.

Tun bayan harin ba-zata da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,200, Isra'ila ta kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a Gaza, inda ta kashe kusan mutum 34,000, mafi yawansu mata da yara, tare da jikkata wasu kusan 77,000.

Yakin da Isra'ila ke yi kan Gaza ya jefa kashi 85 cikin 100 na al'ummar yankin cikin ƙaurace wa gidajensu sakamakon karancin abinci, ruwan sha mai tsafta, da magunguna, yayin da sama da kashi 60 cikin 100 na ababen more rayuwa a yankin suka lalace ko kuma suka lalace, a cewar MDD. da

Ana tuhumar Isra'ila da laifin kisan kiyashi a Kotun Duniya. Wani hukunci na wucin gadi da aka yanke a watan Janairu ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da ayyukan kisan ƙare dangi, tare da daukar matakan tabbatar da cewa ana ba da taimakon jinƙai ga fararen hula a Gaza.

TRT World