Za mu mayar da martani daidai gwargwado kan hare-haren PKK — Ma'aikatar Tsaron Turkiyya

Za mu mayar da martani daidai gwargwado kan hare-haren PKK — Ma'aikatar Tsaron Turkiyya

Rundunar Sojin Turkiyya ta kawar da ƴan ta'addan PKK/YPG 11 a arewacin Syria.
Turkiyya ta shafe sama da shekara 35 tana yaƙi da ƴan ta'adda na PKK. / Hoto: AA

Rundunar Sojin Turkiyya ta “kawar da” ƴan ta’addan PKK/YPG 11 waɗanda aka gano a arewacin Syria, kamar yadda Ma’aikatar Tsaro ta Turkiyya ta sanar.

“Ƴan ta’addan PKK/YPG 11 waɗanda ke shirin kai hari kan rundunonin Olive Branch da Euphrates a arewacin Syria an kawar da su,” kamar yadda ma’aikatar ta sanar a shafinta na X a ranar Litinin.

“Mun ci gaba da mayar da martani daidai gwargwado kan hare-haren ƴan ta'addan,” kamar yadda ta ƙara da cewa.

Hukumomin Turkiyya suna amfani da kalmar “kawar da” domin nuna cewa ƴan ta’addan da ake magana a kai ko dai sun yi saranda ko an kashe su ko kuma an kama su.

Tun daga 2016, Ankara ta yi nasarar ƙaddamar da tsare-tsare uku na yaƙi da ta’addanci a iyakokinta da ke arewacin Syria domin daƙile taruwar ƴan ta’adda da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan.

Rundunonin sun haɗa da Euphrates Shield a 2016 da Olive Branch a 2018 da Peace Spring a 2019.

A hare-haren ta'addanci da PKK ta ɗauki shekara 35 tana kaiwa a Turkiyya, Turkiyyar da Amurka da Ingila da Tarayyar Turai sun bayyanata a matsayin ta ta'addanci, ta yi ajalin sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata da yara ƙanana da jarirai.

TRT World