Shugaban Kasar Turkiyya na yanzu na sake neman kujerar da yake kai karkashin jam’iyyar AKP, inda ‘yan adawa kuma suka tsayar da Kemal Kilicdaroglu shugaban jam’iyyar CHP a matsayin dan takararsu.
A yanzu, mutane da dama sun zaku don su ga yadda jadawalin zaben zai kasance.
Jam’iyyu 36 ne za su shiga zaben tare da fafatawa da juna da suka hada da jam’iyyar Adalci da Cigaba (AKP) da Jam’iyyar Gwagwarmayar ‘Yan Rajin Kishin Kasa (MHP) da Jam’iyyar Hadin Kai Mai Girma (BBP) da Jam’iyyar Al’ummar Jumhuriya (CHP) da Jam’iyyar Saadat.
Sai kuma Jam’iyyar DEVA da Jam’iyyar Makoma da Jam’iyyar IYI da Jam’iyyar Kasa da Jam’iyyar Sake Walwala da Jam’iyyar Dimukradiyya da Jam’iyyar Dimukradiyya ta Masu Saukin Ra’ayi da kuma HDP da ta Kwamunisanci.
Hukumar Zabe ta bayar da ranaku da wa’adi don tabbatar da an yi aiki da wasu ka’idoji a lokacin da ake tunkarar zaben.
Ga wasu daga cikin ranaku da wa’adi masu muhimmanci da ya kamata a rike a zukata:
18 ga Maris: Fara ayyukan zabe a hukumance. Mika yarjeniyoyin hadin kai ga Hukumar Zabe ta Koli da ke dauke da sanya hannun shugabannin jam’yyun da suka hade waje guda.
31 ga Maris: Buga jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa na karshe a jaridar gwamnati, kuma za a fara gangamin zabe.
9 ga Afrilu: Wa’adi ga jam’iyyun siyasa su mika sunayen ‘yan takararsu ga hukumar zabe, kuma suna da har zuwa karfe 23:59 don yin korafi.
27 ga Afrilu—9 ga Mayu: ‘Yan kasar Turkiyya da ke kasashen waje za su jefa kuri’a.
14 ga Mayu: Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki. Za a sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka tattara da yamma.
28 ga Mayu: Idan babu dan takarar da ya samu sama da kashi 50 na kuri’un da aka jefa a zagayen farko na zaben, to za a je zagaye na biyu a ranar 28 ga Mayu.
Hukumar Zabe ta ayyana tsakiyar watan Afrilu a matsayin ranar fara gangami da yakin neman zabe.
Abubuwan da aka hana kafin zabe
A jaridar kasa an buga dukkan abubuwan da Hukumar Zabe ta Koli ta haramta a aikata a ranar zabe.
Za a fara zabe da karfe 08:00 tare da kammalawa da yamma.
A ranar zabe ba za a sayar da giya da duk wasu kayayyayaki da ke da dangantaka da barasa ba daga karfe 6 zuwa 12 na dare na ranar zaben.
Babu wani da za a bai wa damar daukar makami illa masu ayyukan tabbatar da tsaro.
A ranar zabe, za a rufe dukkan wasu wuraren shakatawa na jama’a da dakunan shan shayi da wuraren shan gahawa tare da na yanar gizo.
Kafin karfe 6 na yamma, an haramtawa kafafen yada labarai sanar da hasashen yadda sakamakon zabe zai kasance, sharhi ko cewa wani abu game da zaben.
Hukumar zabe ce za ta bayar da bayanai a tsakanin 6 da 9 na dare game da sakamakon zaben.
Ta yaya wadanda girgizar kasa ta shafa za su yi zabe?
Hukumar Kula da yawan Jama’a da Harkokin Zama Dan Kasa ta bayyana daukar dukkan matakan da suka kamata don tabbatar da mutanen da girgizar kasa ta rutsa da su sun yi zabe.
Har nan da watan Maris wadanda girgizar kasa ta rutsa da su za su iya mika bayanansu ta yanar gizo ga ofisoshin hukumar na yankunan da suka koma bayan afkuwar ibtila’in.