Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Turkiyya ranar 14 ga watan Mayu. / Hoto: AA

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya caccaki kafafen watsa labaran yammacin duniya wadanda kwanakin baya suka yi yunkurin sauya ra'ayin jama'a game da zaben Turkiyya da za a yi ranar 14 ga watan Mayu.

"Me dukkan mujallun suka wallafa a matsayin babban labarinsu? 'Dole Erdogan ya sauka.' Haka (Wadanda aka wallafa) a Jamus, Faransa da Ingila suka ce. Me hakan ke gaya muku?" tambayar da Erdogan ya yi kenan a yayin wani taro a Istanbul ranar Juma'a.

"Ta yaya za ka wallafa irin wadannan kalamai a babban shafin mujalla? Ba ku ne kuka dauki matakin ba, Yammacin Duniya! Mutanen kasata ne za su yanke hukunci kan hakan."

Ya yi tsokacin ne bayan mujallar Birtaniya ta The Economist ta wallafa labari a shafinta na farko game da shugaban Turkiyya inda ta yi kira da a "ceto dimokuradiyya," "Dole Erdogan ya sauka" da kuma ku yi "Zabe!"

Su ma mujallun Le Point da L'Express na kasar Faransa sun wallafa labaran kyamar Erdogan a manyan shafukansu.

Za a gudanar da zaben shugaban Turkiyya da na 'yan majalisar dokoki ranar 14 ga watan Mayu.

Za a fafata ne tsakanin Erdogan, Kemal Kilicdaroglu, na babbar jam'iyyar hamayya ta Republican People's Party (CHP) da kuma gamayyar ATA Alliance da ta tsayar da Sinan Ogan. Shi kuma Muharrem Ince, ya janye daga takarar ranar Alhamis.

Erdogan ya soki Kilicdaroglu

Kazalika Erdogan ya soki Kilicdaroglu bisa ikirarin da ya yi cewa Rasha tana yin katsalandan a zabukan kasar.

"(Kilicdaroglu ya ce) Rasha tana murde zabukan Turkiyya. Wannan abin kunya ne!"

"Idan na ce 'Amurka na tsoma baki a zabukan Turkiyya, Jamus tana tsoma baki, Faransa tana tsoma baki, Ingila tana tsoma baki, me kai (Kilicdaroglu) za ka ce?" in ji shugaban kasar.

Shugaban kasar ya ce ya kwashe shekara 20 yana mu'amala da wadannan kasashe sannan ya tambayi Kilicdaroglu: "Sau nawa ka taba hulda da su" Yaya aka yi ka sansu?"

Ranar Alhamis Kilicdaroglu ya zargi Rasha da watsa wani bidiyo da ke sukar 'yan takarar shugaban kasa a zaben da ke tafe.

TRT World